Gwamnan Neja Ya Dauki Mataki kan Malamin Musulunci da Ke Wa'azi Irin Na Boko Haram
- Gwamnatin Neja ta dakatar da dukkanin ayyukan wani malamin addinin Musulunci da ake zargin yana yada akidar Boko Haram
- Shugaban hukumar kula da harkokin addinai ta Neja, Umar Faruk, ya sanar da cewa an mika rahoton malamin ga jami'an tsaro
- Sheikh Faruk ya ce wani kwamiti da aka kafa ya gano cewa malamin ba shi da ilimin addini kuma yana barazana ga tsaron jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Neja - Gwamnatin jihar Neja ta sanar da cewa za ta mika rahoton wani malamin addinin Musulunci da ake kira da Muhammad Bin Muhammad ga jami'an tsaro.
Gwamnatin ta ce ta dakatar da dukkanin ayyukan malamin yayin da jami'an tsaro za su bincike shi kan zargin da ake yi masa na yaɗa 'aƙidar Boko Haram'.
Shugaban hukumar kula da harkokin addinai ta Neja, Umar Faruk, ya shaidawa BBC Hausa cewa gwamnatin jihar ta gudanar da bincike kan ayyukansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An binciki malami mai wa'azin Boko Haram
Sheikh Faruk ya ce kwamitin da aka kafa don duba batun ya gayyaci malamin, inda suka tattauna da shi kuma suka gano cewa ba shi da cikakken ilimin addini.
An ce malamin yana gudanar da karatuttuka a garin Tafa da ke jihar Neja, inda ya mallaki makarantar Islamiyya tare da mabiya masu halartar darussansa.
Sheikh Faruk ya ce binciken ya nuna cewa hanyoyin da malamin ke bi da aƙidar da yake yaɗawa suna da hatsari ga tsaron jihar Neja da na ƙasa baki ɗaya.
An dakatar da malami mai akidar Boko Haram
Shugaban hukumar ya ce:
"Saboda haka ne aka yanke shawarar dakatar da shi tare da rufe makarantarsa har sai hukumomin tsaro sun kammala bincike."
Haka kuma, an gano cewa malamin yana kira ga magoya bayansa da su guji duk wani abu da ya shafi zaɓuka da dimokuraɗiyyar kasar nan.
Malamin dai ya jawo cece-ku-ce da dama a yankin arewacin Najeriya saboda kalamansa kan sauran malaman addinin Musulunci a yankin.
Alakar Boko Haram da Salafiyya, Izala
A wani labarin, mun ruwaito cewa Alex Thurston, mataimakin farfesa a jami'ar Georgetown, ya ce Boko Haram na da alaka da kungiyoyin Salafiyya da Izala a Arewacin Najeriya.
Mista Alex ya ce Amurkawa na kallon Sheikh Ja'afar Mahmud Adam (marigayi) a matsayin wanda jagoran Boko Haram, Muhammad Yusuf ya samu ilimi a wajensa.
Asali: Legit.ng