Alakar Boko Haram da Salafiyya da kuma Izala a Najeriya
Alex Thurston, mataimakin farfesa ne a tsangayar nazarin harkokin kasashen waje ta jami'ar Georgetown University, ya kuma rubutu a kan asalin kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram a Najeriya da kuma alakarta da Salafiyya a arewacin Najeriya.
Ga fassarar tsakure na daga abin da ya rubuta
A mataki na kasa da kasa, kungiyar mayakan ta Boko Haram ta zamto mafi shaharar siffofin Salafiyya a Najeriya. Duk da haka Boko Haram dan wani burbushi ne na Salafiyya a arewacin kasarnan.
Yawanci 'yan Salafiyya su kan kalubalanci sauran musulmi da kiristocin Najeriya, amma kuma ba mayaka bane 'yan salafiyya ba sa shiga tashin hankali, ba su yarda da korar gwamnatin da ba ta addini ba ko kuma su yi watsi da ilimin zamani.
KU KARANTA KUMA: Abun al'ajabi: Ku kalli hotunan yarinyar da bishiya ke tsiro a jikinta
A littafin na kwanannan, na fadi cewa, Salafiyya ta fi Boko Haram taka rawar gani wajen taimaka wa musulman arewacin Najeriya fahimtar musulunci.
Salafiyya musulmai ne 'yan sunni wanda a ganinsu ita ce kadai hanyar dai dai ta aiwatar da musulunci. Ta kunshi amfani da Qur'ani da sunnar Annabi Muhammadu da ta qarni ukun farko da su ka biyo bayansa (Salaf).
Salafiyya ba sa ragawa Shi'a da sufanci da sauran dariku. A wajen 'yan Salafiyya, salafanci ya na wakiltar tataccen musulunci na al'ummar farko, amma masana tarihi su na ganin abin da ake kira salafiyya ya fara ne daga karni na 20 yayin da wahabiyancin Saudiyya ya samu gamayya da akidun musulunci daga Masar da India da sauransu.
Salafiyya ta zo arewacin Najeriya ne a wajen shekarun 1960 da 1970 ta hannun Abubakar Gumi (1924-1992), wanda ya yi aiki a matsayin babban alkalin musulunci a Arewa daga 1962-1966 daga baya kuma ya zama shahararren mai wa'azi a radio.
Da tasirin makarantar 'yan mulkin mallaka na Ingila,ya fara ganin yawancin malaman gida a matsayin koma baya, Gumi ya zama babban mai suka ga Sufanci.
A shekarar 1978, mabiya bayan Gumi su ka kafa kungiyar Izala da zummar fatattakar kirkirarrun alamura a a musulunci.
Izala ta zama wata kakkarfar cibiyar yaki da sufanci. Amma duk da haka Izala ta samu matsala musamman bayan mutuwar Gumi. A shekarun 1990s Izala ta dare gida 2, daya a Jos dayar kuma a Kaduna.
Bayan haka, matasan masu wa'azin Izala da su ka yi karatu a jami'ar musulunci ta Madina a Saudiyya su ka fara dawowa gida. Wasu daga cikinsu ba su gamsu da Izala ba: inda su ke ganin kungiyar ta maida hankali ga ababe marasa muhimmanci.
KU KARANTA KUMA: An rufe kantin shoprite a Kano kan haraji
A shekarun 1990s, wasu daga cikin daliban na Madina su ka fara gabatar da kansu a Ahlussunna wal jama'a. Wadannan dalibai su na so jama'a su daina kallonsu a matsayin 'yan Izala kawai. amma a matsayin wakilan tsantsar musulmai 'yan sunni.
Mafi shuhura daga cikin wadancan dalibai shi ne Ja'far Adam (1961-2007), wanda ya fito daga gidan talakawa ya zama mafi shaharar malaman Salafiyya a arewacin Najeriya bayan Gumi. Bayan ya dawo daga Madina a shekarar 1993, Adam ya dabbaka wani tsarin salafiyya da ya kasance na Malanta da siyasa.
Shigarsa siyasa ta faru ne bayan jihohin arewacin Najeriya sun fara aiwatar da shari'ar Musulunci a shekarar 1999. Adam ya yi aiki a gwamnatin Kano, duk da cewa ya ajiye aikin a 2005, inda ya ce ba a aiwatar da shariar yanda ya kamata.
An kashe Ja'afar Adam a shekarar 2007 kuma har yanzu ba warware matsalar kisan ba. Idan aka ji sunan Ja'adar a Amurka yawanci ana alakanta shi da horon da jagoran Boko Haram Muhammad Yusuf (1970-2009) ya samu a wajensa.
Rikicin Ja'afar da Yusuf kamar wani sabatta juyatta ne a sha'anin Salafiyya a arewacin Najeriya. Yusuf ya dauki salon wa'azin Ja'far .
Ya yi amfani da haka wajen ruguje ilimin boko. Shi kuma Ja'far ya afka masa da martani ta hanyar kokwanton zurfin ilimin shi Yusuf.
Adam ya yi bayani cewa wa'azi ne ya fi dacewa ba daukar makami ba sannan ya fadi dalilin da ya sa ilimin Boko ke da amfani ga musulmi.
Ku aiko da ra'ayinku dangane da wannan bincike a shafinmu na Facebook a http://www.facebook.com/naijcomhausa ko kuma a Tuwita a http://www.twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng