Boko Halal: Yadda aka kirkiri wani littafi mai yaki da akidun Boko Haram a jihar Borno
- Wata gidauniya mai zaman kanta ta kirkiri wani littafi ta sanya masa suna Boko Halal a jihar Borno
- An buga littafin ne domin koyar da akidu masu kyau sabanin tsauraran ra'ayi irin na 'yan Bko Haram
- An bayyana yadda za a sanya littafin a makarantu domin kawo ci gaba a bangarori da yawa ilimin addini
Gidauniyar Allamin Foundation for Peace, wata kungiya mai zaman kanta (NGO) da ke Maiduguri, jihar Borno, a ranar Lahadi, 10 ga Oktoba, ta gabatar da littafi mai suna ‘Boko Halal’, littafin da aka rubuta don yakar akidun masu tsatsauran ra’ayi.
Da farko an rubuta littafin Boko Halal da harshen Turanci amma yanzu an gajartashi kana da fassara shi zuwa harsunan Hausa da Kanuri, HumAngle ta ruwaito.
Sunan littafin, wanda ke nufin ilimin Boko ba haramun bane, kai tsaye yana kalubalantar tsauraran akidun ta'addanci na Boko Haram.
Hamsatu Allamin, Babbar Darakta na Gidauniyar Allamim, wacce ta jagoranci gabatarwar, ta ce an daidaita littafin na Boko Halal a kololuwar rikicin da aka shafe shekaru 12 ana fuskanta don yada sahihan sakon Musulunci.
Littafin mai shafuka 160 yana dauke da surori 10 yana koyar da zaman lafiya wanda ke inganta hakuri, zaman lafiya cikin lumana, hakazalika da karfafa kafa kungiyoyin zaman lafiya a makarantun Islamiyya.
Allamin ta ce
"An fara tunanin kirkirar wannan jagorar ta zamani ne don rushe labarin Boko Haram, zuwa ga Boko Halal, don haka ta kalubalanci labarin tsattsauran ra'ayi a cikin al'ummar mu."
Boko Halal an fara kirkirar sa ne a shekarar 2016 kuma gidauniyar ta duba shi tare da hadin gwiwar kungiyar Makeiyya, tare da tallafi daga International Civil Society Action Network (ICAN) a karkashin Asusun Zaman Lafiya na IPF.
Duba kananan yara da masu akida mai kyau wacce bata jirkita ba don koyar da su addinin Islama yana daya daga cikin hanyoyin da za a iya bi don dakile sake aukuwar tashin hankalin da ke ci wa jihar tuwo a kwarya shekaru 12 da suka gabata.
Allamin ta kara cewa, za a rarraba littafin ga wasu makarantun Islamiyya guda 20 a cikin Karamar Hukumar Maiduguri da karamar hukumar Jere.
A cewarta:
"A cikin kowane makarantu 20, mun zabi malamai biyar da aka horar da su kan gina zaman lafiya, kuma za mu tallafa musu don kafa kungiyoyin zaman lafiya a Islamiyyarsu inda dalibai 50, za su kasance membobi,"
Hukumar Ilimin Firamare ta Jihar Borno ta yi alkawarin daukar littafin, inda zai zama wani bangare na darasin koyar da zaman lafiya a jihar.
Dr Kullima, sakataren zartarwa na Hukumar Ilimin Firamare ta Jihar Borno, ya ce:
"Wannan ci gaba ne abin maraba kuma za mu duba cikinsa don ganin yadda gwamnati za ta hada gwiwa da gidauniyar don samar da shi don amfani da shi ko da a makarantunmu na yau da kullum ne."
Dr Abba Bukar, wanda ya jagoranci kwamitin bitar littafin ya ce abubuwan da ke kunshe a littafin sun samo asali ne daga ayyukan bincike da yawa, daga koyarwar Alkur'ani mai girma da Hadisi, inda aka ambaci batutuwan zaman lafiya, juriya, da rayuwar addini mai tsarki.
An gano yada saturaran akidu daga batattun malamai na daya daga cikin abubuwan da ke ta'azzara akidar Boko Haram.
Gwamna Zulum ya ba DSS umarnin kame malamai masu wa'azi ba tare da izinin gwamnati ba
Jaridar Punch ta rahoto cewa, gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya umarci jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da su kamo duk wani malamin da ke wa’azi a fili tare da tunzura jama’a kan junan su.
Gwamnan, ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa da masu ruwa da tsaki a taron tattaunawa kan yanayin tsaro na jihar wanda ya samo asali daga mika wuya na daruruwan mayakan Boko Haram a gidan gwamnati ranar Lahadi a Maiduguri.
A cewar gwamnan:
“Wani muhimmin abu da nake son tattaunawa anan shine batun wa’azi a jihar. Idan ba a kula ba, wannan zai zama babban lamari saboda na ji masu wa'azi daban-daban sun fara cin zarafin juna."
Kano: Gwamna Ganduje ya gargadi malamai kan yin wa'azin batanci
A wani labarin, Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya gargadi malaman addinin Islama da su daina yin kalamai masu tayar da hankali, wadanda za su iya keta zaman lafiya, yayin wa’azi, The Guardian ta ruwaito.
Ganduje ya yi wannan kiran ne a ranar Alhamis a Kano lokacin da ya gana da Limamai na Masallacin Juma’at da sauran malaman addinin Musulunci a jihar.
Ya tunatar da malamai matsayinsu a cikin al'umma, yana mai cewa ya kamata su yi iya kokarinsu ko yaushe su zama abin koyi na fatar baki ko a aikace.
Asali: Legit.ng