Durotaye: An Gano Tsohon Hadimin Tinubu da Ya Yi Aikin Watanni 6 ba Tare da Albashi ba

Durotaye: An Gano Tsohon Hadimin Tinubu da Ya Yi Aikin Watanni 6 ba Tare da Albashi ba

  • Tsohon hadimin Shugaba Bola Tinubu, Fela Durotoye ya bayyana cewa ya yi wa gwamnati aiki na wata shida ba tare da albashi ba
  • Fela Durotoye ya tabbatar da cewa ya yi aiki matsayin mataimaki na musamman kan martabar kasa da yi wa jama'a adalci
  • Daga Oktoba 2023 zuwa Maris 2024 da ya yi aiki, Fela Durotoye ya ce bai karbi ko sisin gwamnati ba, kudinsa yake kashewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Fela Durotoye, wani fitaccen mai magana a bainar jama’a, ya bayyana cewa ya yi aiki a gwamnatin Bola Tinubu na tsawon watanni shida ba tare da albashi ba.

A watan Oktoba 2023, Shugaba Tinubu ya naɗa Durotoye a matsayin mataimaki na musamman kan martabar kasa da yiwa jama'a adalci.

Fela Durotoye ya yi magana kan aikin da ya yiwa Tinubu ba tare da karbar albashi ba
Fela Durotoye ya ce bai taba karbar albashi ba a lokacin da ya ke hadimin Tinubu. Hoto: @feladurotoye, @PBATMediaCentre
Asali: Twitter

Wani jadawalin sunayen mutum 13 da ya bazu a kafafen sada zumunta ya nuna Durotoye a cikin hadiman shugaba Tinubu ta fuskar sadarwa, inji rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Surutun Bwala ya jawo masa, an fayyace matsayin hadimin a gwamnatin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Ban karbi albashi ba' - Tsohon hadimin Tinubu

A cikin wata makalar ra'ayi da Fela Durotoye ya wallafa, ya bayyana cewa aikinsa a matsayin mataimaki ga Shugaba Tinubu ya ƙare a watan Maris din 2024.

Ya bayyana cewa a watanni shida da ya kwashe yana yi wa Tinubu aiki, bai karɓi albashi, alawus ko wani tallafi daga gwamnati ba.

Fela Durotoye ya ce ya yi aiki a matsayin mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan martabar kasa da yi wa jama'a adalci daga Oktoba 2023 zuwa Maris 2024.

Durotoye ya kafawa Tinubu sharadin aiki

Kafin ya amince da wannan aiki, ya gindaya sharadin cewa ba zai karɓi albashi ba, domin ya ɗauki aikin a matsayin gudunmawarsa ga ƙasa.

A tsawon watannin da ya kwashe yana aikin, bai karɓi kuɗin gwamnati ba kuma bai nemi gwamnatin ta dawo masa da kudin da ya kashe ba.

Durotoye ya ce da kudin aljihunsa da kuma taimakon iyalansa ne ya biya kuɗin hayar gidan da ya zauna ciki, man fetur, wutar lantarki, da sauran buƙatunsa.

Kara karanta wannan

'Ana shirin bautar da mu,' Kwankwaso ya gano makircin da Legas ke kullawa Arewa

Durotoye ya roki 'yan Najeriya kudi

A baya, Legit Hausa ta rahoto cewa Fela Durotoye, ya roki 'yan Najeriya da su taimaka su yi karo karon kudi domin ya sayi fom din tsayawa takarar shugaban kasa.

Fela Durotoye na daya daga cikin wadanda suka nuna sha'awar tsayawa takarar shugaban kasar Najeriya a zaben 2019, inda ya ke neman tikiti a jam'iyyar ANN.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.