'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Mutum 4 Ƴan Gida Ɗaya a Arewa, Suna Neman N30m
- Rahoto ya nuna cewa wasu gungun 'yan bindiga sun kai farmaki garin Kasangwai da ke karamar hukumar Kagarko ta Kaduna
- Wani shugaban yankin ya ce 'yan bindigar sun sace wani Alhaji Saleh Adamu tare da matarsa da ’ya’yansa biyu yayin farmakin
- A ranar Asabar ne aka ce 'yan bindigar sun kira waya, suka bukaci a kai masu N30m kudin fansar mutanen 4 da suka dauka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Wasu ‘yan bindiga sun harbe wani dan banga tare da yin garkuwa da wasu mutum hudu 'yan gida daya a jihar Katsina.
Rahoto ya nuna cewa 'yan bindigar sun kai farmakin da sace 'yan uwan ne a garin Kasangwai dake karamar hukumar Kagarko ta Kaduna.
'Yan bindiga sun sace mutum 4
Wani shugaban al’ummar yankin ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Daily Trust inda ya ce lamarin ya faru a ranar Alhamis da misalin karfe 10:43 na dare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce 'yan bindigar sun dura gidan wani Alhaji Saleh Adamu yayin da suka kai hari Kasangwai, inda suka tafi da shi tare da matarsa da ’ya’yansa biyu.
Shugaban ya ce 'yan bindigar sun farmki Alhaji Adamu wanda ke sana’ar shanu jim kadan bayan dawowarsa daga kasuwar kauyen SCC da ke karamar hukumar Kachia.
Kudin fansa: 'Yan bindiga na neman N30m
A cewarsa, wasu ’yan banga sun kai daukin gaggawa tare da yin musayar wuta da 'yan bindigar amma aka ci karfinsu, lamarin da ya yi silar mutuwar dan banga daya.
Ya ce an tuntubi wadanda suka sace Alhajin da iyalansa a ranar Asabar da misalin karfe 5:12 na yamma kuma sun nemi Naira miliyan 30 matsayin kudin fansa.
An kasa samun tabbacin faruwar lamarin daga bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur, har ya zuwa lokacin mika rahoton.
Mutum 4 sun mutu a harin 'yan bindiga
A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan bindiga sun halaka mutum hudu tare da yin garkuwa da wasu da dama a wani hari da suka kai Kauran Namoda a jihar Zamfara.
An ce harin 'yan bindigar na zuwa ne mako daya bayan da suka sako wasu mazauna yankin Dogon Kade mutum 46 bayan da aka biya N21m kudin fansa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng