Da duminsa: Ƴan bindiga sun sace mutum 5 ƴan gida ɗaya, sun nemi a biya N10m

Da duminsa: Ƴan bindiga sun sace mutum 5 ƴan gida ɗaya, sun nemi a biya N10m

- Wasu yan bindiga sun sace maigidanci da matarsa da yaransa uku a hanyar Ajowa Akoko

- Magidancin, Ibrahim Olusa, da iyalansa na hanyarsu na komawa Abuje ne bayan hutun Easter

- Majiya daga iyalan ta tabbatar da cewa masu garkuwar sun nemi a biya su naira miliyan 10 kudin fansa

'Yan bindiga sun sace mutane biyar yan gida daya a yankin Ajowa Akoko a jihar Ondo yayin da suke hutun bikin Easter, Vanguard ta ruwaito.

A halin yanzu, wata majiya daga iyalan ta ce masu garkuwan sun tuntube su suna neman a biya su naira miliyan 10 kudin fansa kafin su sako wadanda suka sace.

Da duminsa: Ƴan bindiga sun sace mutum 5 ƴan gida ɗaya, sun nemi a biya N10m
Da duminsa: Ƴan bindiga sun sace mutum 5 ƴan gida ɗaya, sun nemi a biya N10m. Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

Majiyar Legit.ng ta gano cewa wanda aka sace din mai suna Ibrahim Olusa, dan asalin Daja Ajowa, da matarsa da yaransa uku an sace su ne tsakanin Ajowa Akoko da Ayere a jihar Kogi.

DUBA WANNAN: Kabir: Ɗan Nigeria da bai taɓa karatun Boko ba ya ƙera babura a Katsina

Iyalan suna hanyarsu ta komawa Abuja ne bayan sun gama hutun Easter a garinsu na Ajowa.

Sace su da aka yi ya tada hankulan mutane inda yanzu suke zaman dar-dar.

Wata majiya daga iyalan ya shaidawa manema labarai a Akure cewa masu garkuwar sun tuntube su sun nemi a biya naira miliyan 10.

Tsohon shugaban karamar hukumar Ajowa Akoko, Ajayi Bakare ya ce rashin kyawun titi ne ke janyo yawaitar fashi a hanyar Ajowa Ayere.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun kashe shugaban 'yan bindiga da ake nema ruwa a jallo a Zamfara

Bakare ya yi kira ga gwamnati ta taimaka ta gyara hanyar garin domin inganta zirga-zirgar motocci.

Kakakin yan sandan jihar, Tee Leo Ikoro ya ce har yanzu ba a sanar da shi afkuwar lamarin ba.

Majiyar Legit.ng ta gano cewa an sanar da shugaban Amotekun na jihar, Adetunji Adeleye afkuwar lamarin kuma ya tura jami'ai.

A wani rahoton daban, Fadar Shugaban Kasa a ranar Lahadi ta ce kalaman Bishop din Katolika na Jihar Sokoto, Mathew Kukah, basu yi kama da na malamin addini ba a sakon sa na bikin Easter inda ya soki shugaban kasa, Muhammadu Buhari da gwamnatinsa.

Babban mai taimakawa shugaban kasa bangaren yada labarai, Garba Shehu, shine ya bayyana haka a wata sanarwa mai taken "kalaman Kukah kan Buhari rashin adalci ne," The Punch ta ruwaito.

Shehu ya ce tunda dai Kukah ya ce shi malami ne, bai kamata ya dauki bangaranci wajen yin adalci da fadar gaskiya ba.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel