Yan bindiga sun sace yan gida daya su 17 a Kaduna

Yan bindiga sun sace yan gida daya su 17 a Kaduna

- Masu garkuwa da mutane sun sace mutum 21 a kauyen Udawa da ke karamar hukumar Chikum, jihar Kaduna

- Daga cikin wadanda aka sace akwai yan gida daya su goma sha bakwai

- An kuma jikkata wasu da dama a harin da aka kai a ranakun Juma'a da Asabar

Rahotanni sun kawo cewa yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 21 a kauyen Udawa da ke karamar hukumar Chikum na jihar Kaduna.

Lamarin ya afku ne a lokuta biyu mabanbanta a karshen mako, inda 17 daga cikin mutanen da aka sace suka kasance yan gida daya, jaridar The Cable ta ruwaito.

Liman Hussaini, wani jigo a kauyen Udawa wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce wasu yan bindiga da ba a sani ba sun kai mamaya yankin sannan suka fara harbi ba kakkautawa, inda suka raunana mutane da dama.

A cewar Hussaini, an yi garkuwa da mutum hudu a ranar Juma’a, yayinda aka sace sauran 17 a ranar Asabar a hanyarsu ta zuwa gona da misalin karfe 7:00 na safe.

Yan bindiga sun sace yan gida daya su 17 a Kaduna

Yan bindiga sun sace yan gida daya su 17 a Kaduna Hoto: FRCN
Source: UGC

Hakazalika an kwashi wasu mutum hudu daga cikin dangin wadanda aka sace a ranar Asabar zuwa wani asibiti a Kaduna, sakamakon raunukan da suka ji a lokacin harin.

KU KARANTA KUMA: Farashin kayan abinci ya fadi warwas a jihar Taraba, a Kano, Katsina, Benue da Nasarawa abun babu sauki

“A jiya, yan gida daya su 21 na a hanyarsu ta zuwa gona, amma sai yan bindiga suka kai masu hari bayan sun yi tafiyar kimanin kilomita daya da rabi. Hudu daga cikinsu sun ji mugun rauni daga harbi sannan aka sace 17 daga cikinsu,” in ji shi.

“Hakazalika, a ranar Juma’a, da misalin karfe 7:00 na safe, an sace mutum hudu a hanyarsu ta zuwa gona.

“Kun san akwai yunwa sosai. Da kyar mutane ke samun abinci, amma a yanzu da masara yayi, iyalai da yawa sun dogara ne a kan masarar. Mun fara girbe masara wanda muke ci saboda babu abinci.

“Uban wadannan iyalai 21 na tuka kekensa tare da daya daga cikin yaransa maza da yaransa mata biyu zuwa gona lokacin da yan bindigan suka bude masu wuta bayan sun sace mutum 17 cikin iyalan.

“An harbi mutumin a kafarsa; an harbi dan a baki. Harbin ya samu daya daga cikin yara matan a kirji sannan dayar a hannu. An kwashi su duka hudun zuwa asibiti a Kaduna.”

Hussaini ya kara da cewar koda dai an zuba jami’an tsaro a Udawa, “zuwa lokacin da suka kai wajen da lamarin ya afku, yan bindigan sun riga sun gudu cikin jeji tare da mutanen da suka sace.”

Ya yi korafi a kan lamarin tsaro a yankin, inda yace mazauna kauyen za su kamu da yunwa idan basu je gonakinsu ba.

KU KARANTA KUMA: Matar Alaafin Aishat ta ce mijinta ya fi matasa da dama iya tarairayan mace

“Wannan shine abunda ke ta faruwa a garinmu. Zuwa gona babban hatsari ne. A daya bangaren, idan baka je gona ba, yunwa zai kashe ka da iyalanka. Don haka, muna fuskantar abubuwa biyu masu hatsari,” ya kara da cewa.

Ba a samu jin ta bakin kakakin yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige ba saboda wayarsa a kashe take a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

A wani labari na daban, Yan sanda a jihar Abia sun kama mutum huɗu da ake zargi da hannu wurin kisar wani sufetan yan sanda mai suna Princewill Divine.

Kwamishinan ƴan sandan jihar, Misis Janet Agbede ce ta bayyana hakan yayin jawabin da ta yi wa manema labarai a ranar Juma'a a Umuahia kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel