'Ana Shirin Bautar da Mu,' Kwankwaso Ya Gano Makircin da Legas Ke Kullawa Arewa

'Ana Shirin Bautar da Mu,' Kwankwaso Ya Gano Makircin da Legas Ke Kullawa Arewa

  • Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi Legas da shirin yi wa Arewacin Najeriya mulkin mallaka
  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP a 2023 ya ce a Legas ne aka kitsa makircin nada sarki a cikin tsakiyar jihar Kano
  • Kwankwaso ya yi ikirarin cewa Legas na son bautar da Arewa ta hanyar karbe mata haraji, tilasta masu zuba jari zuwa jiharsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP a 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi ikirarin cewa ana shirin yi wa Arewa mulkin mallaka daga Legas.

Kwankwaso ya yi wannan zargin ne a lokacin da ya ke gabatar da jawabi yayin taron dalibai na jami'ar Skyline a Kano, inda ya yi tsokaci kan takaddamar masarautar jihar.

Kara karanta wannan

Ganduje ya rama abin da aka yi masa, ya ki zuwa auren yar Kwankwaso a Kano

Kwankwaso ya yi magana kan makircin da ake kullawa daga Legas na bautar da Arewa
Kwankwaso ya fallasa makircin da ake kullawa Arewa daga Legas na mulkin mallaka. Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Kwankwaso ya magantu kan sarautar Kano

Jaridar Daily Trust ta rahoto Kwankwaso ya ce akwai matsaloli da yawa a Arewa, kamar rashin tsaro, yunwa, talauci, cututtuka da sauransu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, an mayar da sarkin Kano tamkar wani 'abin wasa' a yayin da Arewa ke fama da wadannan matsalolin.

Kwankwaso ya kuma yi ikirarin cewa akwai shirin da ake yi daga Legas na kakaba wanda suke so matsayin sarkin Kano da kuma bautar da jama'ar yankin.

“A yau, muna iya gani a sarari cewa akwai yunƙuri da yawa daga ɓangaren Legas domin yin mulkin mallaka a wannan yanki na ƙasar.
"Yau, Legas ba za ta bar mu mu zabi sarki ba, wai Legas ce za ta zo har tsakiyar Kano domin nada nasu sarkin.”

- A cewar Kwankwaso.

Kwankwaso ya gano wani 'makircin' Legas

Tsohon gwamnan jihar Kanon ya caccaki Legas kan karbar harajin 'yan Arewa inda ya yi ikirarin matasa daga Legas na aiki tukuru domin kwashe albarkatun Kano.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya jero mutane ya musu godiya bayan auren yarsa

The Cable ta ce Kwankwaso ya nuna damuwa cewa harajin da ake karba daga rijistar wayoyin 'talafon' a jihar Kano da Arewacin kasar suna karewa ne a hannun 'yan Legas.

A cewarsa, masu zuba jari a Arewa na samun matsin lamba domin su mayar da hedikwatar kamfanoninsu da bankunansu zuwa jihar Legas, wanda ke nufin kai arziki can.

Ya yi kira ga 'yan majalisu daga Arewa da su tabbatar da cewa ba a tauye hakkin shiyyar ba, tare da kasancewa masu sa ido kan dokokin da ake kafawa a kasar.

"A magance matsalolin Arewa" - Kwankwaso

A wani labarin, mun ruwaito cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bukaci shugabanni su yi aiki tukuru domin gyara matsalolin Najeriya.

Kwankwaso ya ce rashin tsaro, tabarbarewar tattalin arziki da kuma ƙarancin ababen more rayuwa, musamman wutar lantarki, sun zama matsalar Arewa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.