Obasanjo Ya Bukaci Tinubu Ya Kori Shugaban INEC Mahmood Yakubu, Ya ba da Dalili
- Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya caccaki shugaban INEC, Mahmood Yakubu, kan abubuwan da suka faru a 2023
- Obasanjo ya ce akwai bukatar a kori Farfesa Yakubu da sauran jami’an INEC a matakin jiha da kananan hukumomi na kasar nan
- Yayin da ya ba da dalili, tsohon shugaban na Najeriya ya bayyana yadda ya kamata a nada shugaban INEC da wanda ya kamata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi kira da a kori shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu.
Obasanjo ya ce ya kamata a kori jami’an INEC a dukkanin matakai a wani bangare na sake fasalin tsarin zabe a Najeriya.
Obasanjo ya nemi a tsige shugaban INEC
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake magana a wani taron shugabanci na gidauniyar Chinua Achebe a Jami’ar Yale, da ke Amurka, inji rahoton Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da ya nemi a gaggauta tsige Farfesa Mahmood, Obasanjo ya bayyana zaben 2023 a matsayin “wani abu da ya saba hankali.”
Tsohon shugaban na Najeriya ya ce dole ne shugaban hukumar ta INEC ya zama ya fi karfin masu mulki kuma ya kasance wanda ba za a iya juya shi da cin hanci ba.
Obasanjo ya soki amfani da BVAS, IREV
Obasanjo ya ce abin takaici ne yadda shugaban INEC din da kansa ya kawo tsarin amfani da fasahohin BVAS da IREV amma a karshe basu yi amfani ba.
Ya zargi INEC da kin yin amfani da na'urorin a yayin zaben 2023 wanda ya jawo aka samu kura kurai a zaben, lamarin da ya kira 'kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.'
Obasanjo ya kuma yi kira da a rage wa jami’an INEC wa’adi da kuma tsaurara matakan tantancewa domin hana nada ‘yan bangar siyasa.
Obasanjo ya radawa Tinubu sabon suna
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon shugaban ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo ya yi magana kan halin da Najeriya ke ciki a mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Cif Olusegun Obasanjo ya ce lamura sun lalace, kasa ta rikice a cikin watannin da Bola Ahmed Tinubu ya yi a kan karagar mulki inda ya kira shi da 'Baba go slow.'
Asali: Legit.ng