Ganduje Ya Rama Abin da Aka Yi Masa, Ya Ki Zuwa Auren Yar Kwankwaso a Kano
- Manyan yan siyasa da yan kasuwa da dama ne suka halarci bikin auren Dr. Aisha Kwankwaso da dan attajiri, Alhaji Dahiru Mangal
- Mutane da dama na tambayar dalilin da ya sa tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje bai halarci auren yar Rabiu Kwankwaso ba
- Sai dai wasu na hasashen Ganduje ya rama abin da Kwankwaso ya yi masa ne lokacin auren yarsa a shekarar 2018
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - An gudanar da bikin daurin auren yar Sanata Rabiu Kwankwaso a jiya Asabar 16 ga watan Nuwambar 2024.
Manyan mutane da suka hada da yan siyasa da yan kasuwa da malaman addini da dama sun halarci bikin.
Yan siyasa sun halarci auren yar Kwankwaso
Daga cikin manyan yan siyasa akwai mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da Atiku Abubakar da Olusegun Obasanjo, kamar yadda Kwankwaso ya yi musu godiya a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai abin mamaki, an nemi tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje an rasa a wurin bikin da wasu jiga-jigan APC.
Shugaban APC mai mulki a Najeriya bai samu halartar bikin ba kuma bai tura kowa da sunan ya wakilce shi ba a bikin.
Yar Kwankwaso: An yi hasashen rashin zuwan Ganduje
Wasu majiyoyi suna hasashen hakan bai rasa nasaba da aikin jam'iyya da yake yi a ranar wacce ta yi daidai da zaben gwamna a Ondo.
Har ila yau, wasu sun yi hasashen rashin jituwa ne tsakanin Ganduje da Kwankwaso a siyasance zai jawo haka tun bayan samun rashin matsala da Ganduje ya zama gwamnan Kano.
Wasu mutane sun yi bayyana ra'ayoyinsu daban-daban kan lamarin inda wasu ke cewa Ganduje bai je auren ba ne saboda fargabar yi masa rashin mutunci.
Kwankwaso ya fadawa Ganduje baka a auren yarsa
A baya, kun ji yadda Sanata Rabiu Kwankwaso ya caccakawa Abdullahi Ganduje bakar magana kan auren yarsa da ya yi a shekarar 2018.
Kwankwaso ya kwatanta auren yar Ganduje mai suna Fatima da cewa auren 'zawarawa' za a yi ba wani sabon abu ba ne wanda ya jawo maganganu.
Hakan ya jawo ce-ce-ku-ce inda wasu ke ganin bai dace Kwankwaso ya furta irin wadannan kalamai ba ko da kuwa akwai bambancin siyasa.
Asali: Legit.ng