Sanata Kwankwaso ya yi magana game da ta’aziyyar da Ganduje ya zo ya yi masa har gida

Sanata Kwankwaso ya yi magana game da ta’aziyyar da Ganduje ya zo ya yi masa har gida

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya zanta da manema labarai bayan gwamnan Kano ya yi masa ta’aziyya
  • Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya je gidan tsohon Mai gidansa a kan rasuwar da aka yi masa
  • Sanata Kwankwaso yace ya ji dadin ganin wadanda su ka zo yi masa gaisuwa da masu aiko sakonni

Kano - Tambari TV Hausa tayi hira da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a game da rashin da aka yi masa a farkon makon nan na Inuwa Musa Kwankwaso.

Da yake zantawa da manema labaran, da farko ‘dan siyasar ya fara da maganar rashin ‘danuwa da ya yi, ya na mai yabon Marigayi Inuwa Musa Kwankwaso.

Rabiu Musa Kwankwaso yace daga Ubangiji Madaukakin Sarki muke, kuma gare shi za mu koma. Kwankwaso yace 'danuwan na sa ya samu shaidar mutane.

Kara karanta wannan

Ganduje: A Shirye Na Ke In Yi Sulhu Da Kwankwaso

“Kamar yadda ka fada, a jiya (Litinin) mu ka tashi da wannan babban rashi a wurinmu da ma jama’ar Kano da na tarayya baki-daya domin Alhaji Inuwa ya yi karatunsa a wannan jiha da wajen wannan jiha da kuma kasashen waje.”
“Kuma tun da ya fara aiki, ya yi aiki ne da gwamnatin tarayya, inda ya bada gudumuwa kwarai da gaske a ka nabin da ya shafi gandun daji.”

"Bai shiga siyasa ba, amma ya yi alheri"

“Tun da ya yi ritaya yake zaune a wannan jiha, ba shi da ra’ayi irin na mu na siyasa.
Mun gode Allah, ya yi rayuwa mai kyau, ya yi alheri ga al’umma, wasu abubuwan ma ban sani ba sai da ya rasu nake ji tsakanin jiya da yau, an yi masa shaida a kan yadda yake da alheri.” - Rabiu Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Garin dadi: Bidiyon 'yan sanda na raba wa masu mota kudi maimakon karba daga hannunsu

A karshe Rabiu Kwankwaso wanda ya yi gwamna sau biyu tsakanin 1999 da 2003 da 2011 zuwa 2015 ya yi wa wannan Bawan Allah addu’o’i na cikawa da imani.

Sanata Kwankwaso
Dr. Abdullahi Ganduje da Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: @mohd.saifullahi.9
Asali: Facebook

Zuwan Gwamna gidan babban abokin hamayyarsa

Tsohon Ministan ya roki Allah (SWT) Ya bada lada ga wadanda suka yi wa mamacin addu’a, ya bayyana irin dadin da ya ji saboda ganin mutane sun zo ta'aziyya.

“Mun godewa Allah, a irin wannan yanayi na wannan babban rashi, duk wanda ya zo wannan wuri, ko karami ne ko babba, abin farin ciki ne a wuri na.”
“Duk wanda ya zo zai yi wa wannan mamaci, ya yi wa ‘yanuwa da iyaye addu’a. Ai ka ga wannan babban abu ne.”
“Mun gode ga duk wanda ya zo wannan wuri, da wadanda suke yin waya, da wanda ya turo sako, domin mu fada masu cewa duk wanda ba zai samu daman zuwa ba, ya zauna saboda yanayin da ake ciki (na harkar tsaro).”

Kara karanta wannan

Sarkin Kano zai angwance da galleliyar budurwa, tsohuwar zumansa nan kusa

“Mu na godewa duk wadanda suka zo, da wadanda suka bada duk wata gudumuwa, da ma wadanda suke gidajensu, suka yi addu’a, Allah ya ba su lada.” - Rabiu Kwankwaso.

Akwai sulhu a Kano?

Dazu aka ji Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya ce a shirye ya ke da ya shirya da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bayan sun raba jiha tun 2018.

A wata tattaunawa da Radio France ta yi da shi, gwamnan ya kwatanta rashin jituwar da ta shiga tsakaninsu a matsayin sabanin siyasa da wasu a gefe suka hura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel