Kwankwaso ya maida martini ga auren yar Ganduje, ya yi ba’a ga ma’auratan da sunan “zawarawa”
Ana ci gaba da samun cece-kuce akan bikin auren yar Ganduje da dan Ajimobi, inda tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi Kwankwaso ya bi sahun masu sharhi.
Ganduje ya aurar da dansa Fatima ga Idris Ajimobi, dan gwamnan jihar Oyo, inda akayi biki na gani na fada.
Amma da yake jawabi ga magoya bayansa a Kaduna a ranar Asabar, Kwankwaso yayi ba’a ga ma’auratan, cewa ‘zawarawa’ne.
“Tsirarun mutane ne ke farin ciki da auren zawarawa saboda sun rigada sun zama daya.
“Mun samu labarin cewa yan kudu, yan arewa, yan gabas da kuma yan arewa sun cika Kano domin auren ma’aurata zawarawa.
“A yau Kano ya daidaita saboda wannan aure,” cewar gwamnan.
Ya kuma bayyana cewa manyan masu ruwa da tsaki da suka bar gurin aikinsu don halartan bikin basu da aiki a gabansu.
KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Buhari bata da karfin kare yan Najeriya - Suswam
“Mun kuma samu labarin cewa mutane daga gurare da dama da basu da aiki a gabansu sun bar ayyukansu domin halartan bikin.
“Na kuma samu labarin cewa wannan biki na mutun daya ya dakatar da mutane daga gudanar da harkokinsu.
“Dukka wannan ya nuna banbaci tsakanin amana da rashin amana, tsakanin haske da duhu, tsakanin auren dubban ma’aurata da kuma na ma’aurata guda,” cewar tsohon gwamnan.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng