‘Dan Jarida Ya Taso Kwastam, Ya Fito da Bidiyoyin da ya Tona Yadda Ake Fasa Kauri
- Fisayo Soyombo ya na ta fitar da bidiyoyin da ke zargin kwastam ta na taimakawa wajen fasa kauri a Najeriya
- ‘Dan jaridar ya zargi hukuma da taimakawa masu fasa kauri, ya ce da hannunsu ake shigo da haramtattun kaya
- Soyombo ya ce an nemi ya fadi kudin da yake so a biya shi, zargin da hukumar ta karyata ta bakin wani jami’inta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Lagos - Fisayo Soyombo wanda ‘dan jarida ne mai binciken kwa-kwaf, ya matsawa jami’an kwastam lamba, yana zarginsu da barna.
Fisayo Soyombo ya dade yana tuhumar ma’aikatan kwastam masu kula da iyakoki da taimakawa masu yin fasa kauri a Najeriya.
Rahoton Sahara Reporters ya bayyana cewa Mista Fisayo Soyombo ya fitar da bidiyoyi da ke nuna danyen aikin jami’an kwastam.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abuga: 'Dan jarida ya zargi kwastam da laifi
‘Dan jaridar ya yi ikirarin ‘yan kwastam sun hada kai da wani attajiri, Adeyemi Habeeb Abdulganiy wajen shigo da haramtattun kaya.
A cewarsa, Adeyemi Habeeb Abdulganiy wanda aka fi sani da Abuga ya samu daurin gindin hukuma wajen shigo da motoci da shinkafa.
Soyombo yake cewa a ranar 10 ga watan Nuwamba 2024 aka shigo da motoci 2000 cike da buhunan shinkafa cikin Najeriya ta iyakoki.
Idan batun ya tabbata, kowace mota ta shigo da motoci 65 ta iyakar Najeriya da Benin.
‘Dan jaridar ya shaidawa duniya hanyoyin da za a bi wajen shigo da motocin kuma za a iya amfani da wasu dakarun sojoji a yi aika-aikar.
Kwastam sun karyata Fisayo Soyombo
Jami’in hulda da jama’a na kwastam, Abdullahi Aliyu Maiwada ya karyata zargin ‘dan jaridan, yake cewa labaran kanzon kurege ne.
Ranar Talata bayan an yi wannan sai Soyombo ya sake fito da wasu bidiyoyi biyu da nufin ya tabbatar da gaskiyar abin da yake ta fada.
Idan kuma 'yan kwastam ba su yarda da wannan ba, ya ce a shirye yake ya karo wasu hujjojin.
'Yan kwastam za su ba 'yan jarida cin hanci?
A shafinsa na X, sai ya sake fitowa ya na cewa ‘yan kwastam da masu fasa kaurin kaya su na ta kokarin ganin yadda za su ba shi cin hanci.
A watan Maris ya bayyana cewa an bukaci ya fadi duk kudin da yake so a biya shi, Soyombo ya ce an sake yi masa tayi a cikin Afrilu.
Duk da haka ba a hakura ba, sai ya ce an nemi a biya shi N50m domin ya daina fasa kwai, ya fito ya fadawa ‘yan Najeriya halin da ake ciki.
Kwastam ta karbe miyagun makamai
Kafin yanzu, rahoto ya zo cewa kwastam ta fitar da rahoto kan makaman da ta kama ana shirin shigowa da su cikin jihohin Najeriya.
Hukumar ta ce an yi yunkurin shigowa da makaman na kashi 60% na makaman na sama da Naira biliyan ga miyagun 'yan ta'adda.
Asali: Legit.ng