Kungiyar AIED ta yi Allah-wadai da shirin cafke Fisayo Soyombo
Kungiyar AIED mai wayar da kan jama’a a kan cigaban tattalin arziki a Najeriya ta soki shirin da gwamnatin tarayya ta ke yi a bayan fage na damke fitaccen ‘dan jaridar nan Fisayo Soyombo.
AIED ta bayyana yunkurin da ake yi na cafke Fisayo Soyombo a matsayin burmawa mulkin kama-karya. Kungiyar ta bayyana wannan ne ta bakin wani jami’inta, Kwamred O’Seun John.
A jawabin da Darektan yada labaran kungiyar ya fitar a Ranar Talata 22 ga Oktoba, ya ce: “Mun tashi gari da mummunan labarin da ke iya jefa kasarmu cikin wani yanayi na rashin tsari.”
“Jami’an gwamnatin tarayya sun taso Mista Fisayo Soyombo, babban ‘dan jarida mai binciken kwa-kwaf ya na kan gaba wajen bankado barnar da ake yi a gidajen yari da ofishin ‘yan sanda.”
KU KARANTA: Bola Tinubu ya yi magana game da amfanin ilmi a Najeriya
"Fisayo Sayombo babban gwarzon kasa ne wanda ya jefa kansa a cikin hadari domin ceto kasar nan. Maimakon gwamnatin tarayya ta karkatar da dukiya wajen kama shi, ta bi kan masu laifi.”
AIED tace: “Wannan shirin na cafke shi abin Allah-wadai ne ga kowane wayayye. Kamar yadda Yemi Osinbajo ya fada, ba aikin ‘dan jarida bane ya rahoto abin da wane da wane su ka fada.”
Kungiyar mai zaman kanta, ta kara da cewa: "Osinbajo yace aikin ‘dan jarida shi ne ya yi bincike kuma ya rahoto gaskiya. Fisayo Sayombo ya yi abin da bai kamata a bi shi da mugun nufi ba.”
O’Seun John ya na ganin cewa wannan ‘dan jarida ya cancanci a yaba masa a cikin al’ummarmu. Sayombo shi ne ya bankado irin rashin gaskiyar da ‘yan sanda da gandurobobin kasar su ke yi.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng