Fasa kauri: Jami’an kwastam sun kama wiwi da ta kai N1,000,000,000

Fasa kauri: Jami’an kwastam sun kama wiwi da ta kai N1,000,000,000

Hukumar yaki da fasa kauri ta Najeriya reshen Marine a jahar Legas ta bayyana ta kama haramtattun kaya da aka shigo dasu Najeriya da darajarsu ta kai naira biliyan 1.06.

Punch ta ruwaito hukumar ta ce ta kama kayan ne duka duka a wata ukun farko na shekarar 2020, babba daga cikin kayan shi ne tabar wiwi da darajarsa ta kai naira biliyan 1.

KU KARANTA: Duk wanda ya shiga yajin aiki a bakacin aikinsa – El-Rufai ga jami’an kiwon lafiya

Kwanturola Olugboyega Peters ne ya bayyana haka, inda yace wannan shi ne mafi tsadar kayan da hukumar ta kama tun da aka kafata, wanda hakan na nufin aikin yaki da fasa kauri ya karu.

Kaakakin reshen, Emmanuel Tangwa ya bayyana cewa a yayin yaki da fasa kaurin sun kama kayayyki 39 a farkon shekarar 2020, ba kamar shekarar 2019 ba inda suka kama kaya 12.

Fasa kauri: Jami’an kwastam sun kama wiwi da ta kai N1,000,000,000
Jami’an kwastam
Asali: Depositphotos

Da yake bayani Tangwa yace sun kama buhun shinkafa 1,816 da harajinsu ya kai N38.13m, kwali 733 na naman kaji da harajinsu ya kai N7.42m da buhun wiwi 196 da kudinsu ya kai N1bn.

Sauran sun hada da dila 104 na gwanjo da harajinsu ya kai N4.39m, dilan atamfofi 655 da kudin harajinsu ya kai naira miliyan 2.09, litan mai 112 da harajinsu ya kai N112,000.

Haka zalika akwai dila 25 na gwajon takalma da igiyar daure wando da suka kai darajar naira miliyan 8.02, sai kwalin cingam guda 25 da kudin harajinsu ya kai naira miliyan 1.2.

Kakaaki Tangwa yace wannan shi tabar wiwi mafi yawa da hukumar ta taba kamawa a wannan hanya a tarihinta gaba daya duba da lokacin da aka kama kayan.

Ya danganta karin kayan da suka kama ga jajircewa da ma’aikatan hukumar suke nunawa a bakin aiki domin cimma manufofin kafa hukumar, tare da nuna ingancin dabarun aikinsu.

A wani labari, Hasashe na tsimi da tanadi da hukumar kiddiga ta Najeriya ta gudanar ya nuna tattalin arzikin Najeriya zai shiga halin tabarbarewa da kashi -4.4 saboda annobar Coronavirus.

Premium Times ta ruwaito ministar kudi, Zainab Ahmad ce ta bayyana haka ga manema labaru bayan kammala taron majalisar tattalin arzikin kasa daya gudana a ranar Alhamis.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng