NNPC: Najeriya za Ta Yi Aiki da Kasashen Waje 2 a Gano Dalilin Faduwar Jirgin Sama
- Ministan harkokin sufurin jirgin sama, Festus Keyamo ya bayyana cewa ana binciken dalilin faduwar jirgin NNPCL
- Jirgin 'East Wind' da kamfanin ya dauko haya ya fadi a jihar Ribas dauke da mutane da yawansu bai gaza takwas ba
- Yanzu haka Najeriya na aiki da kasashen Amurka da Faransa domin bankado musabbabin faduwar jirgin a kwanaki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Rivers - Ministan harkokin sufurin jirgin sama na kasa, Festus Keyamo ya ce Najeriya ta nemi tallafin kasashen Amurka da Faransa kan faduwar jirgin NNPCL.
A ranar 28 Oktoba ne jirgin 'East Wind' da kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya dauko hayarsa ya fadi a jihar bayan tasowarsa daga Fatakwal.
Jaridar The Cable ta wallafa cewa jirgin na dauke da fasinjoji shida da ma'aikatan jirgi biyu a lokacin da ya fadi, inda aka gano wasu gawarwaki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Najeriya ta fara binciken faduwar jirgin NNPCL
Jaridar The Guardian ta wallafa cewa gwamnatin kasar nan ta fara binciken abin da ya jawo faduwar jirgin da kamfanin NNPCL ya dauko haya.
An gano gawarwaki hudu jim kadan bayan faduwar jirgin, yayin da aka gano gawa ta biyar bayan mako guda da faduwarsa, tare da kwanson bayanan jirgin da ake kira da 'black box.'
Faduwar jirgi: Dalilin dauko Amurka da Faransa
A zantawarsa da manema labarai a Abuja, Ministan harkokin sufurin jirgin sama, Festus Keyamo ya ce jami'an kasar nan za su hadu da na Amurka da Faransa kan faduwar jirgin sama.
Festus Keyamo ya ce an sako kasashen biyu cikin binciken ne domin an kera jirgin a Amurka, amma injin dan Faransa ne.
An samu karin gawar ma'aikacin NNPCL
A baya kun ji cewa ofishin bincike da ba da kariya na kasa ya bayyana cewa an kara gano gawar daya daga cikin ma'aikatan kamfanin mai na kasa (NNPCL) bayan faduwar jirgi a Ribas.
Daraktar hulda jama'a da kare hakkin abokan hulda, Bimbo Oladeji ta ce an gano karin gawa guda wanda aka kai dakin adana gawa bayan mako guda da faduwar jirgin saman a jihar Ribas.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng