EFCC: 'Yadda Wani Gwamna a Najeriya Ya Tura Miliyoyin Naira Zuwa Asusun Ɗan Canji'
- Wani ɗan canji, Ayuba Tanko ya bayyana yadda gwamnatin Anambra karkashin Willie Obiano ta musanya kudi zuwa Dala a wurinsa a 2017
- EFCC ta gabatar da Ayuba a matsayin shaida na biyar a gaban Mai Shari'a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya a ƙarar da ake tuhumar Obiano
- Shaidan ya ce gwamnatin Obiano ta tura masa N416m a asusu daga baya ta karbi Dalolin Amurka kwatankwacin wannan kudi a lokacin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Anambra - Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziki ta'adi watau EFCC ta ci gaba da gabatar da shaidu kan tuhumar da takewa tsohon gwamnan Anambra, Willie Obiano.
Wani ɗan kasuwar canji watau BDC, Ayuba Tanko ya gurfana a gaban Mai shari'a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya mai zama a Abuja a matsayin shaidar EFCC na biyar.
A rahoton Daily Trust, Ayuba Tanko ya ce a lokacin da Obiano ke mulkin Anambara, ya yi amfani da wakili wajen tura N416m zuwa asusun kamfaninsa a 2017.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
EFCC: Yadda gwamna ya canji Daloli
Ya shaidawa alkali cewa an turo kudin lokaci daban-daban kuma daga baya aka musanya su zuwa Dalar Amurka miliyan 1.137 kwatankwacin Naira miliyan 416.
Ayuba ya ce:
"Ni ɗan kasuwa ne, ina musayar kudi kamar Dalar Amurka, Yuro, da sauransu. Ina da kwastomomi wani lokacin kuma na kan zama ɗan tsakani na samu lada."
Adadin kudin da gwamna ya turawa ɗan canji
Shaidan ya kara da cewa yana amfani da kamfanonin canji guda biyu wajen tafuyar da kasuwancinsa, sun haɗa da Sauki Bureau De Change da Zigaziga Trading.
Lokacin da babban lauyan hukumar EFCC ya tambaye shi ko nawa ya karba a lokacin, ɗan canjin ya ce:
"A tsakanin watan Afrilu 2017 zuwa Disamba 2017, an turo mun jimillar kuɗi Naira miliyan 416 kuma na ba da dala kwatankwacinsu watau $1,137,000.00."
Ayuba ya ce wannan ne kaɗai kasuwancin da ya haɗa shi da gwamnatin Anambra a karkashin Gwamna Obiano, babu wani bayan shi.
Lauyan Obiano, Onyechi Ikpeazu, SAN, ya tambayi shaidan ko ya taba yin mu’amala da tsohon gwamnan kai tsaye, Ayuba ya ce: “Ban yi hulda kai tsaye da wanda ake kara ba.”
EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan Kwara
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kwara a gaban kotu.
EFCC ta shigar da sababbin tuhume-tuhume a kan Abdulfatah Ahmed da kwamishinansa na kuɗi kan zargin karkatar da N5.78bn.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng