Lakurawa: Dakarun Sojojin Sama Sun Sheke 'Yan Ta'adda Masu Tarin Yawa
- Dakarun sojojin saman Najeriya sun kai hare-hare kan maɓoyar ƴan ta'adda a jihohin Kebbi da Zamfara
- Jami'an tsaron sun hallaka ƴan ta'adda masu tarin yawa ciki har da na sabuwar ƙungiyar Lakurawa da ta bayyana a cikin ƴan kwanakin nan
- Sojojin sun kuma lalata ma'ajiyar makaman shugaban ƴan bindiga Ado Aleiro tare da hallaka mayaƙansa a jihar Zamfara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Dakarun sojojin saman Najeriya sun hallaka ƴan ta'adda masu yawa a wasu dazuzzukan da ke tsakanin jihohin Zamfara da Kebbi.
An tattaro cewa ƴan ta’addan, waɗanda wasu daga cikinsu ƴan ƙungiyar Lakurawa ne, an kashe su ne a wani wuri da ake kira Sangeko a Zamfara, kusa da kan iyaka da jihar Kebbi.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an kashe wasu daga cikin ƴan ta’addan a sansanin Ado Aleiro, yayin da aka lalata wasu sansanoni na manyan shugabannin ƴan bindiga daban-daban.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojojin sama sun sheƙe ƴan ta'adda
Da yake tabbatar da hakan a ranar Lahadi, mai magana da yawun NAF, Olusola Akinboyewa, ya bayyana cewa an kai hare-haren ne bayan samun bayanan sirri.
Olusola Akinboyewa ya kuma bayyana cewa, an kai harin bam a sansanin Ado Aleiro da ke kusa da tsaunin Asola a ƙaramar hukumar Tsafe a ranar Juma’a, rahoton Tribune ya tabbatar.
"A ranar 8 ga Nuwamba, 2024, dakarun NAF sun kai wani harin ba-zata a sansanoni da dama, ciki har da wurin da ake kira Sangeko a Zamfara, kusa da kan iyaka da Kebbi."
"...da kuma sansanin Ado Aleiro da ke kusa da tsaunin Asola a ƙaramar hukumar Tsafe."
"Hare-haren ba wai kawai sun lalata wata babbar ma’ajiyar makamai mallakar shugaban ƴan bindiga, Ado Aleiro ba ne, sun halaka da yawa daga cikin mayaƙansa."
- Olusola Akinboyewa
Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin saman Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) sun kai hare-hare kan sansanonin ƴan ta'addan ISWAP.
Dakarun sojojin saman sun kai hare-haren ne a kudancin tafkin Chadi, lamarin da ya yi sanadiyyar kashe ƴan ta'adda masu yawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng