Malami Ya Tono Badakalar Naira Biliyan 40 da Aka Yi a Majalisa a Kasafin 2024

Malami Ya Tono Badakalar Naira Biliyan 40 da Aka Yi a Majalisa a Kasafin 2024

  • Bashir Aliyu Umar ya zargi ‘yan majalisar tarayya da cigaba da yin cushen ayyuka a kundin kasafin kudin kasa
  • Malamin addinin musuluncin ya bayyana yadda kasafin wata makaranta a jihar Legas ta koma N40bn daga N600m
  • Dr. Bashir Umar ya bukaci mutane su dage da addu’o’i domin Ubangiji ya kawo karshen halin da ake ciki a yau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Bashir Aliyu Umar ya koka a game da yadda abubuwa suke tafiya a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da ke mulki.

Fitaccen malamin addinin ya yi magana a kan sha’anin tattalin arziki, ya nuna takaici kan zargin badakalar cushe a kasafin kudi.

Majalisa
Ana zargin 'yan majalisa da cushe a kasafin kudin 2024 Hoto: Aso Rock Villa/House of Representatives, Federal Republic of Nigeria
Asali: Facebook

Bashir Aliyu Umar ya zargi majalisa da cushe

A wani bidiyo da Dr. Abubakar Hidima ya wallafa a dandalin X kwanan nan, an ji Bashir Aliyu Umar ya na tir da majalisar tarayya.

Kara karanta wannan

"Shi ne mafi alheri" Sanata a Arewa ya fito da manufar cire tallafin mai a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin ya ce babu abin da ya tada masa hankali kamar yadda aka kumbura kasafin kudin makarantar koyon kiwon kifi da ke Legas.

"Su kasafin kudin da suka kai, N630bn, amma mutanen nan – ‘yan majalisa suka maida shi Naira biliyan 40 da ‘yan kai.
"‘Yan kan ma sun fi karfin kasafin kudin da suke bukata. Kuma a lokacin Janar Muhammadu Buhari abin ya soma bayyana."

- Dr. Bashir Aliyu Umar

Tarihin cushe a kasafin kudi a majalisar tarayya

Sheikh Bashir Aliyu Umar ya ce a mulkin Muhammadu Buhari aka fara fahimtar ana yin cushen ayyuka a cikin kasafin kudin kasa.

Tun ‘yan majalisar tarayya suna yin kari kadan a boye a kasafin kudi, shehin ya ce yanzu ta kai lamarin ya kazanta a zamanin nan.

Badakalar N40.21bn a kasafin kudin 2024

Kara karanta wannan

Gwamna a Arewa zai kashe N93bn a samar da ruwa, zai biya ma'aikata bashin N800m

Wannan makaranta ta bukaci ta kashe N667m a kundin kasafin 2024, amma sai majalisa ta kara adadin kudin zuwa N40.88bn.

BudgetIT mai bibiyar kudin da ake kashewa a Najeriya ya fallasa yadda ‘yan majalisar tarayya suka yi cushe-cushe a kasafin.

Ana zargin an cusa abubuwa 160 wadanda makarantar ba ta san da zamansu ba lokacin da aka kai wa majalisa kasafin na bana.

Bashir Aliyu Umar ya ce a yi ta addu'a

Shawarar da malamin ya kawo ita ce a dage da addu’a, domin ana tsoron a karshe ‘yan majalisa ne suke wawaso da dukiyar jama’a.

Masanin hadisin na Manzon Allah SAW ya ce addu’a ce kurum mafita kuma Ubangiji SWT ya na amsa rokin bawan da aka zulunta.

'Dan majalisar da ke sukan Bola Tinubu

A baya an ji labarin yadda Sanatan Kudancin Borno ya fito baro-baro ya fadawa shugaban kasa cewa an katange shi a Aso Villa.

Kwanan nan Sanata Mohammed Ali Ndume ya soki kara kudin man fetur duk da ya rasa mukaminsa a majalisa a dalilin kalamansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng