FBI Ta Cafke Sabon Shugaban Karamar Hukuma a Najeriya kan Damfarar $3.3m

FBI Ta Cafke Sabon Shugaban Karamar Hukuma a Najeriya kan Damfarar $3.3m

  • Sabon shugaban karamar hukuma a jihar Anambra, Franklin Ikechukwu Nwadialo ya shiga hannun jami'an hukumar FBI
  • An cafke Nwadialo ne saukarsa ke da wuya a filin tashi da saukar jirage a Texas da ke ƙasar Amurka
  • Ana zargin dan siyasar mai shekaru 40 da damfarar $3.3m da wasu tuhume-tuhume guda 13 a kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Texas, Amurka - Hukumar FBI da ke Amurka ta cafke wani shugaban karamar hukuma a Najeriya.

Hukumar FBI ta cafke Franklin Ikechukwu Nwadialo wanda sabon shugaban karamar hukumar Ogbaru ne a jihar Anambra.

FBI ta kama shugaban karamar hukuma kan zargin damfara
Hukumar FBI ta cafke shugaban karamar hukuma a jihar Anambra. Hoto: Hon. Franklin Ikechukwu Nwadialo, FBI - Federal Bureau of Investigation.
Asali: Facebook

Nwadialo ya ci zaɓen shugaban karamar hukuma

USA Today ta ruwaito cewa ana zargin Nwadialo da damfarar $3.3m da wasu tuhume-tuhume guda 13.

Kara karanta wannan

Ana daf da zabe, yan APC sun watsawa Gwamna kasa a ido, sun goyi bayan dan adawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan wanda ake zargin ya yi nasara a zaben kananan hukumomi da aka gudanar a jihar Anambra.

An gudanar da zaben ne a ranar 28 ga watan Satumbar 2024 inda jam'iyyar APGA mai mulkin jihar ta lashe suka kujeru 21, cewar Daily Trust.

Har ila yau, hukumar zaben jihar ta ce APGA ce ta kuma lashe duka kujerun kansiloli da aka yi inda APC da PDP ba su tashi da komai ba.

Zarge-zarge kan sabon shugaban karamar hukuma

Hukumar FBI ta ce idan aka tabbatar da zargin, Nwadialo zai iya fuskantar daurin shekaru 20 a gidan kaso.

An cafke Nwadialo ne mai shekaru 40 bayan ya isa kasar Amurka inda za a wuce da shi yankin Yammacin Washington domin gurfanar da shi.

Kara karanta wannan

Damfarar $3.3m: Gwamnati ta yi magana kan cafke dan siyasar Najeriya a Amurka

Nwadialo yana yawan amfani da sunaye daban-daban wurin damfarar musamman mata a kafofin sadarwa.

Mafi yawan lokuta yana cewa shi soja ne kuma ba zai iya zuwa wurin wadanda yake mu'amala da su ba inda wani lokaci suke tura masa kudi.

FBI ta gano wanda ya kuskuri Trump

Kun ji cewa Hukumar FBI ta bayyana Thomas Matthew Crooks a matsayin wanda ya kai harin kisan gilla kan tsohon shugaban kasar Donald Trump.

An ce Thomas Crooks, dan shekaru 20 ya kasance dan jam'iyyar Republican ne kamar yadda bayanan kada kuri'arsa suka nuna.

Kakakin hukumar FBI, Anthony Guglielmi ya ce jami'in leken asirin Amurka ne ya harbe wanda ake zargin bayan kai harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.