Rundunar Ƴan Sanda Za Ta Tura Jami'ai 22000 Zuwa Kudancin Najeriya, An Gano Dalili

Rundunar Ƴan Sanda Za Ta Tura Jami'ai 22000 Zuwa Kudancin Najeriya, An Gano Dalili

  • Sufetan 'yan sanda na kasa (IGP), Kayode Egbetokun, ya sanar da tura jami'ai 22,239 zuwa Ondo domin ba da tsaro a zabe
  • Egbetokun ya bayyana cewa 'yan sanda za su aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin gudanar da zabe cikin lumana
  • Ya kuma nuna damuwa kan wasu jam'iyyun siyasa da ke tayar da tarzoma, wanda zai iya kawo barazana ga tsaron zaben

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaban rundunar 'yan sanda na kasa (IGP), Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa za a tura jami'ai 22,239 zuwa jihar Ondo.

Kayode Egbetokun ya nuna cewa jami'an da za a tura za su tabbatar da tsaro yayin zaben gwamna a jihar na ranar 16 ga Nuwamba.

Kara karanta wannan

Bauchi: Kotu ta ɗauki matakin hukunta tsohon da ya wallafa hotunansa da ƴan mata

IGP Kayode Egbetokun ya yi magana kan tura jami'an 'yan sanda zuwa jihar Ondo
Rundunar 'yan sanda za ta tura jami'ai 22,000 zuwa jihar Ondo gabanin zabe. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

'Yan sanda sun shiryawa zaben Ondo

IGP ya bayyana hakan ne a taron masu ruwa da tsaki kan zaben gwamnan jihar Ondo da aka gudanar a Akure a ranar Alhamis, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Egbetokun ya ce jami'an za su yi aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da isasshen tsaro da kariya a cikin kananan hukumomi 18 na jihar.

The Punch ta rahoto cewa Egbetokun ya samu wakilcin mataimakin sufeta janar na 'yan sanda (AIG), shiyya ta 17, Abiodun Asabi, a taron.

'Yan sanda sun zargi jam'iyyun siyasa

A cewar Egbetokun, zaben yana daga cikin muhimman tsare-tsaren dimokuradiyya wanda ke ba 'yan kasa damar zaben shugabanninsu ta hanyar kada kuri'a.

Ya bayyana cewa nasarar zaben gwamna mai zuwa a jihar Ondo ta ta'allaka ne akan zaman lafiya, shirin jami'ai da kuma tsaron da aka samu lokacin zaben.

Kara karanta wannan

DHQ: Dakarun sojoji sun samu babbar nasara, sun kashe ƴan bindiga sama da 400

Egbetokun ya zargi wasu manyan jam'iyyun siyasa da ci gaba da kara jawo tashin hankali a cikin al'umma, wanda ke haifar da barazanar tsaro kafin zaben.

Sarki ya goyi bayan dan takarar APC

A wani labarin, mun ruwaito cewa fitaccen basarake a jihar Ondo, Oba Olufaderin Adetimehin, ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar APC, Lucky Aiyedatiwa.

Sarki Adetimehin ya bukaci masu zabe a jihar Ondo da su kada kuri’unsu ga Gwamna Lucky Aiyedatiwa a zaben jihar na ranar 16 ga Nuwamba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.