Menene Gaskiyar Rade Radin Mutuwar Rochas Okorocha? Hadiminsa Ya Yi Magana
- Hadimin tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya yi martani kan rade-radin cewa Sanatan ya bar duniya
- Ebere Nzeworji ya musanta labarin da ake yaɗawa a jiya Laraba, ya ce Okorocha lafiyarsa kalau babu abin da ke damunsa
- Hakan ya biyo bayan yada jita-jitar cewa Sanata Rochas Okorocha ya rasu a birnin Landan da ke Birtaniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Imo - An yi ta yaɗawa a kafofin sadarwa cewa tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha ya kwanta dama.
Sai dai hadiminsa, Ebere Nzeworji ya ƙaryata labarin da ake yaɗawa cewa sanatan ya rasu a birnin Landan.
An musanta labarin rasuwar Rochas Okorocha
Nzeworji ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa a yau Alhamis 7 ga watan Nuwambar 2024, cewar rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hadimin sanatan ya ce Okorocha yana nan cikin koshin lafiya babu ko ciwon kai da ke damunsa.
Ya ce labarin da ake yaɗawa tun da safiyar jiya Laraba kan rasuwar Rochas Okorocha babu kamshin gaskiya a ciki.
Har ila yau, Nzeworji ya fayyace cewa a daidai lokacin da ake yaɗawa cewa ya rasu, Okorocha na birnin Abuja bayan dawowa daga Owerri.
Okorocha ya halarci tarurruka a Abuja da Imo
Daga bisani Nzeworji ya ce Okorocha ya halarci bikin binne marigayi Cif Emmanuel Iwuanyanwu a ranar Juma'a 1 ga watan Nuwambar 2024.
Nzeworji ya ce sanatan ya kuma gana da mataimakin shugaban Majalisar Wakilai, Hon. Benjamin Kalu da wasu 'yan Majalisar a gidansa da ke Owerri.
"Abin mamaki ne yadda mutane ke yada irin wannan labarin, sai ka rasa dalilinsu na yin haka."
"Sanata Okorocha mutum ne da ya yi aiki a matakin jiha da na Tarayya wanda ya ke da abokai da dama masu mutunci."
"Tsohon gwamnan bai taba yi wa wani fatan mutuwa ba kullum a cikin fara'a yake da al'umma."
- Ebere Nzeworji
Gidan Rochas Okorocha ya rushe a Abuja
Kun ji cewa gidan tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha ya ruguje wanda ya jefa mazauna kusa da gidan cikin zullumi.
Rahotanni sun ce ana tsaka da gyaran gidan mai hawa biyar a lokacin da ya fadi, kuma ya danne mutane da dama a birnin Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng