Ajali Ya Yi Kira, Mutum Sama da 20 Sun Rasu da Iftila'i Ya Afka Masu a Jihohi 2

Ajali Ya Yi Kira, Mutum Sama da 20 Sun Rasu da Iftila'i Ya Afka Masu a Jihohi 2

  • Mutane 22 masu haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba sun rasa rayukansu da ƙasa ta danne su a yankunan Adamawa da Taraba
  • An ruwaito cewa lamarin ya faru a gandun dajin da ya haɗa ƙaramar hukumar Gashaka ta Adamawa da Toungo a Taraba
  • Bayanai sun nuna cewa ana yawan rasa rayuka a wurin saboda haƙar ma'adanai ta haramtacciyar hanya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Adamawa - Akalla mutane 22 ne ake kyautata zaton sun mutu da wani ramin haƙar ma'adanai na haram ya rufta a jihohin Adamawa da Taraba.

Lamarin ya afku ne a wani gandun daji na ƙasa da ya haɗa ƙaramar hukumar Gashaka a jihar Adamawa da Toungo a jihar Taraba duk a Arewa maso Gabas.

Kara karanta wannan

Wani bom ya tarwatse da mutane a babbar kasuwa a Najeriya, an rasa rayuka

Wurin hakar ma'adanai.
Ramin hakar ma'adanai ya rufta kan mutane 22 a Adamawa da Taraba Hoto: Contributor
Asali: Getty Images

Mutum sama da 20 sun rasu a ramin

Daily Trust ta ce wani mai hakar ma’adinai ya bayyana cewa da yawa daga cikin wadanda suka rasu sun fito ne daga garin Jamtare da ke karamar hukumar Gashaka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutumin mai suna, Adamu Jamtare ya ce:

"Suna hakar zinare a wani yanki da ake kira Buffa a gandun dajin Gashaka-Gumti, wanda ya haɗa Gashaka da Toungo. duka mutane 22 da suka makale a ramin ana kyautata zaton sun mutu,”

Ana zargin har da ƴan Zamfara a ramin

Shugaban karamar hukumar Toungo, Injiniya Suleiman Toungo, ya tabbatar da cewa an gano gawarwakin mutum biyar duk da cewa bai da tabbacin adadin da aka binne.

Ya ce lamarin, wanda ake zargin ya rutsa masu hakar ma’adinai daga sassa daban-daban na Najeriya da suka hada da Zamfara da Adamawa ya faru kusan wata guda da ya gabata.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya dauki mataki kan yaran da aka tsare saboda zanga zanga

Yadda rami ke halaka masu haƙar ma'adanai

An tattaro cewa ana yawan rasa rayuka a ƴan shekarun nan a gandun dajin wanda aka sani da albarkatun ma'adanai, jaridar Pulse ta ruwaito.

Wani ɗan kauyen Tila da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce kusan masu haƙar ma'adanai 70 suka mutu a bara amma galibi ba a fitar da rahoton lamarin ba.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya tabbatar da mutuwar mutane 22 a baya-bayan nan.

Rami ya danne mutane a Zamfara

Ku na da labarin mutum uku sun kwanta dama bayan wani ramin haƙar ma'adanai ya rufto kan ma'aikata a Zamfara.

Ramin wanda ya rufto a ƙaramar hukumar Anka ta jihar ya kuma yi sanadiyyar jikkata rayukan mutum 11 a lokacin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262