Dakatar da Dan Majalisa Ya Bar Baya da Kura a Jihar Delta
- Majalisar dokokin jihar Delta da ke yankin Kudu maso Kudu ta ɗauki matakin ladabtarwa kan ɗaya daga cikin mambobinta
- Majalisar Delta ta dakatar da mamban da ke wakiltar mazaɓar Ukwuani, Chukudi Dafe, bisa zarginsa da aikata ba daidai ba
- Dakatarwar da aka yi wa ɗan majalisar ya jawo ce-ce-ku-ce saboda ƙin bayyana takamaiman laifin da ake zarginsa da aikatawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Delta - Majalisar dokokin jihar Delta ta ɗauki matakin dakatar da ɗaya daga cikin mambobinta.
Majalisar ta dakatar da ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Ukwuani, Chukudi Dafe, bisa zarginsa da aikata ba daidai ba.
Meyasa aka dakatar da ɗan majalisa a Delta?
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Injiniya Emeka Nwaobi ne ya gabatar da ƙudirin dakatarwar na kwanaki 14, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƙudirin ya samu goyon bayan babban mai tsawatarwa, Perkins Umukoro, rahoton Daily Post ya tabbatar da zancen.
Nan take aka zartar da ƙudirin ba tare da wani ƙarin haske ba game da takamaiman zargin da ake yi wa Chukwudi Dafe.
Dakatar da ɗan majalisa ya jawo cece-kuce
Majiyoyi a cikin majalisar sun bayyana cewa dakatarwar ta tayar da jijiyar wuya a tsakanin ƴan majalisar.
Wasu daga cikinsu ba su ji daɗin yadda shugabannin majalisar suke tafiyar da harkokin ladabtarwa na cikin gida ba.
Duk da kiraye-kirayen da aka yi na a fayyace gaskiya, shugabannin majalisar sun ƙi bayyana cikakkun bayanai kan takamaiman zargin aikata ba daidai ɗin da ake yi wa ɗan majalisar ba.
Dakatarwar dai ta haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin ƴan siyasar jihar Delta, inda masu lura da al’amura suka buƙaci majalisar ta riƙa bayyana harkokinta na cikin gida ba ɓoye-ɓoye ba.
Jam'iyyar APC ta dakatar da ɗan majalisa
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta reshen jihar Zamfara ta dakatar da ɗan majalisar wakilan tarayya, Aminu Sani Jaji.
Jam'iyyar APC ta bayyana cewa ta ɗauki wannan matakin kan ɗan majalisar ne bisa zarginsa da cin amana da yi wa jam'iyya zagon ƙasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng