Jam'iyar APC ta dakatar da Hon. Muhammad Gudaji Kazaure

Jam'iyar APC ta dakatar da Hon. Muhammad Gudaji Kazaure

- Jam'iyyar APC ta dakatar da Hon. Muhammad Gudaji Kazaure mamba mai wakiltar mazabar Kazaure, Roni, Gwiwa da Yankwashi a majalisar wakilai

- An dakatar da Kazaure na tsawon watanni shida sakamakon wani rubutu da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta

- Shugaban jam'iyyar na karamar hukumar Kazaure, Hassan Lawan ne ya tabbatar da hakan

Jam’iyyar All Progressives Congress APC, reshen karamar hukumar Kazaure a jihar Jigawa ta dakatar da mamba mai wakiltar mazabar Kazaure, Roni, Gwiwa da Yankwashi a majalisar wakilai, Muhammad Gudaji Kazaure.

Hakan na kunshe ne a cikin wata takardar dakatarwa da jaridar Daily Post ta samu dauke da sa hannun shugaban jam'iyyar, na karamar hukumar Kazaure, Hassan Lawan.

KU KARANTA KUMA: FG ta bayyana dalilin da yasa Buhari ya nada Yahaya a matsayin shugaban hafsan soji

Jam'iyar APC ta dakatar da Hon. Muhammad Gudaji Kazaure
Jam'iyar APC ta dakatar da Hon. Muhammad Gudaji Kazaure Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Ya ce an dakatar da dan majalisar tarayyar na tsawon watanni shida saboda wani rubutu da ake zarginsa da wallafawa a shafinsa na Facebook da Twitter a kan gwamnan jihar Muhammad Badaru Abubakar wanda ya saba wa doka ta 21 (ii) da (v) na kundin tsarin mulkin APC.

Ya bayyana cewa dakatarwar ta biyo bayan dakatarwar da shugabannin yankinsa na Yamma suka yi a can baya.

Hassan ya ce bisa koke-koken da aka karba daga yankin dan majalisar ne shugabannin zartarwar Jam’iyyar na Karamar Hukumar suka yi taron gaggawa kuma suka yanke shawara biyu.

Shawarwarin sun hada da kafa kwamitin ladabtarwa na mutum bakwai don bincikar zargin tare da gabatar da rahoto cikin kwanaki goma yayin da aka dakatar da dan majalisa na tsawon watanni shida har zuwa lokacin da za a gudanar da bincike.

KU KARANTA KUMA: Hatsarin jirgin ruwan Kebbi: An gano gawawwaki 76 kawo yanzu

A cikin rubutun nasa, Gudaji ya zargi Gwamna Badaru da gabatar da sunayen shuwagabanni da kansiloli ‘yan takarar zaben kananan hukumomi mai zuwa ba tare da zaben fidda gwani ba ko wata yarjejeniya kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyya ya jagoranta.

Jaridar Daily Nigerian Hausa ma ta tabbatar da dakatarwar da aka yi wa dan majalisar a shafinta na Facebook.

A wani labarin, Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya soke majalisar zartarwa na jiharsa nan take, The Nation ta ruwaito.

Sakataren gwamnatin jihar, SSG, Keneth Ugbala ne ya sanar da soke majalisar bayan taronta a ranar Juma'a a Abakaliki.

Amma ya ce akwai wasu masu rike da muhimman mukamai da abin bai shafe su ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel