Sweden: Kotu Ta Daure Dan Gwagwarmaya a Gidan Kaso kan Kona Alkur'ani, Ya Yi Martani
- Wata kotu a kasar Sweden ta daure dan gwagwarmaya Rasmus Paludan a gidan kaso kan cin zarafin Musulunci da musulmai
- Kotun ya daure matashin mai suna Paludan har na tsawon watanni hudu a gidan gyaran hali kan kona Alkur'ani a 2023 a ƙasar
- Hakan ya biyo bayan kalaman batanci kan Musulunci a zanga-zangar da aka yi Kudancin birnin Malmo tun a shekarar 2022
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Malmo, Sweden - Kotu a kasar Sweden ta yanke hukunci ga wani dan gwagwarmaya da ya kona Alkur'ani mai girma.
Kotun ta yi hukuncin ne a yau Talata 5 ga watan Nuwambar 2024 inda ta daure shi tsawon watanni hudu a gidan kaso.
An daure matashi da ya kona Alkur'ani a Sweden
Reuters ta ce Rasmus Paludan dan kasar Denmark wanda ya zo kasar yawon bude ido ya yi kakkausar suka ga musulmai yayin zanga-zanga a 2022.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga bisani ya kona Alkur'ani a ofishin jakadancin Turkiyya da ke Stockholm a Sweden a watan Janairun 2023.
A watan Agusta masu gabatar da kara suka gurfanar da shi a gaban kotu kan tuhume-tuhume da suka hada da kiyayyar kabilanci a birnin Malmo.
Yayin zanga-zangar, Paludan ya yi ta maganganu marasa dadi ga Musulmai da kuma kona Littafinsu mai tsarki.
An kuma zarge shi da nuna kiyayya da kalaman banza ga Larabawa da kuma yan Nahiyar Afirka cewar Bloomberg.
Abin da alƙalin kotun ya fada
Alƙalin kotun, Nicklas Soderberg ya ce ya hallata mutum ya soki wasu mutane ko addinisu amma bai kamata ya wuce gona da iri ba.
Ya ce kalamansa sun wuce muhawara sai dai cin zarafi da neman bata sunan Musulunci da Musulmai.
Sai dai Paludan ya ki amincewa da zargin da ake yi masa, ya ce kawai ya soki Musulmai ne da kamfe ga jam'iyyarsa ta Stram Kurs.
Gwamnatin Sweden ta magantu kan kona Alkur'ani
A baya, mun ba ku labarin cewa gwamnatin kasar Sweden ta yi Allah wadai da kona Alkur'ani mai girma a kasar, ta ce babu hannunta a ciki.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta fitar inda ta ce hakan ya sabawa dokokin kasar.
Ta ce babu muhallin wariyar addini ko na launin fata da kabilanci a kasar, inda ta ce kone duk wani littafi mai tsarki laifi ne.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng