Rikici ya barke a kasar Sweden sakamakon shirya taron kona Al-Kur'ani da wasu sukayi

Rikici ya barke a kasar Sweden sakamakon shirya taron kona Al-Kur'ani da wasu sukayi

Rikici ya barke yayin zanga-zanga a garin Malmo, kudancin kasar Sweden sakamakon shirya kona Al-Kur'ani mai girma da wasu masu ra'ayin rikau sukayi, Yan sanda sun bayyana ranar Asabar.

Hukumomi sun bayyana cewa masu zanga-zanga kimanin 300 sun kona tayoyi tare da jifan yan sanda yan sa'o'i bayan an hana wani dan siyasa makiyin addini Musulunci halartan taron kona Al-Kur'ani.

Wasu yan ra'ayin rikau suka dauki kansu suna kona Al-Kur'ani kuma suka daura a yanar gizo don cin fuskan Musulmai, kakakin yan sanda, Rickard Lundqvist ya bayyanawa jaridar kasar Sweden Expressen.

Daga baya, yan sanda Sweden sun damke mutane uku da ake zargi da laifin yunkurin tayar da zaune tsaye ta hanyar kwallo da Al-Kur'ani mai girma.

Wani dan siyasan kasar Denmark, Rasmus Paludan, wanda ke da'awar kiyayya da baki ya shirya halartan wani taro a garim Malmo a ranar Juma'a.

Amma jami'an tsaro suka rigashi zuwa wajen kuma suka sanar da cewa an haramta masa shigowa kasar Sweden na tsawon shekaru biyu. Daga baya aka damkeshi.

"Munyi hasashen zai karya doka a Sweden," Calle Persson, kakakin hukumar yan sandan garin Malmo ya bayyana AFP.

"Hakazalika akwai yiwuwan halinsa na da barazana ga al'umma."

Amma magoya bayansa suka cigaba da taron duk da an kamashi, inda aka damke mutane uku cikinsu.

Rikici ya barke a kasar Sweden sakamakon shirya taron kona Al-Kur'ani da wasu sukayi
Rikici ya barke a kasar Sweden sakamakon shirya taron kona Al-Kur'ani da wasu sukayi
Source: UGC

Daga bayan Pauldan ya rubuta a shafin Facebook dinsa cewa: "An koreni kuma an hana ni shiga Sweden na tsawon shekaru biyu. Amma an amincewa makasa da masu fyade shiga."

Zaku tuna cewa a bara, Pauldan ya tayar d kura inda ya kona Al-kur'ani.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel