Gwamnati Ta Soke Kwangilar N740bn, Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna Ya Tsaya Cak

Gwamnati Ta Soke Kwangilar N740bn, Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna Ya Tsaya Cak

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta soke kwangilar da ke tsakaninta da kamfanin Julius Berger (MJB) ta Naira biliyan 740
  • A makon da ya gabata ne gwamnati ta nemi kamfanin MJB da ya kara aikin gina titin Abuja-Kaduna a kan Naira biliyan 74.79
  • Sai dai kamfanin ya ki tabuka komai game da aikin titin har karewar wa'adin da aka deba masa, lamarin da ya sa aka soke kwangilar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya sanar da cewa ta soke kwangilar Naira biliyan 740 na aikin gina babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Gwamnatin ta bayyana cewa ta soke kwangilar aikin daga hannun Julius Berger (MJB) saboda gaza tabuka abin kirki daga kamfanin.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fadi nasarar da ya samu a watanni 17 bayan ya gaji Buhari

Gwamnati ta yi magana yayin da ta soke kwangilar titin Abuja-Kaduna daga Julius Berger
Gwamnati ta soke kwangilar da ta ba kamfanin Julius Berger na gina titin Abuja-Kaduna. Hoto: @realdaveumahi, @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Gwamnati ta soki tsarin aikin kamfanin JB

Channels TV ta rahoto cewa minsitan ayyuka, David Umahi ya zargi kamfanin Julius Berger (MJB) da yi wa aikin hanyar rikon sakainar kashi domin bata sunan gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya nuna cewa a watan jiya, Umahi ya bukaci kamfanin JB ya karbi tayin gwamnati na N740.79bn domin kammala kilomita 82 na zango na biyu na gina titin.

Duk da cewa gwamnatin tarayya ta amince da fitar da kudin, ministan ya ce kamfanin ya ki yin wani abin kirki, yayin da ya ke ta jan kafa wajen aiwatar da aikin.

Gwamnati ta soke kwangilar titin Abuja-Kaduna

A wata sanarwa da daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar ayyuka ta tarayya Mohammed Ahmed ya fitar a ranar Litinin ya ce:

"An dakatar da kwangilar ne bayan da wa'adin da aka debawa kamfanin na kammala aikin ya kare a ranar Litinin, kuma dama an sanar da su matakin dakatarwar."

Kara karanta wannan

Zanga zanga ta barke a hedikwatar NNPCL, Mele Kyari ya shiga tsaka mai wuya

Ma'aikatar ta kuma ce ta yi tattaunawa daban-daban da kamfanin tsawon watanni da dama, amma tattaunawar ta kasa haifar da wani da mai ido.

An kusa gama aikin titin Abuja-Katsina

A wani labarin, mun ruwaito cewa ministan ayyuka, David Umahi ya ba da tabbacin cewa za a kammala aikin gina titin Abuja-Kaduna-Kano-Katsina nan da karshen shekarar 2025.

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa kamfanin Dangote, BUA da Julius Berger ne za su yi aikin kuma ana sa ran kammala titin Sokoto zuwa Badagry a kan lokaci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.