Yadda Hadiza Bala Usman Ta Samu Wuka da Nama Wajen Yanka Ministocin Tinubu

Yadda Hadiza Bala Usman Ta Samu Wuka da Nama Wajen Yanka Ministocin Tinubu

  • A lokacin mulkin Muhammadu Buhari ne Hadiza Bala Usman ta rasa kujerar da ta ke kai ta shugabar hukumar NPA
  • ‘Yar siyasar ta taya Bola Tinubu kamfe a zaben 2023, daga nan kuma ta sake samun wani mukami mai tasiri sosai
  • A yau idan Hadiza Bala Usman ta na iya yin sanadiyyar da minista zai rasa matsayinsa a gwamnatin Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Hadiza Bala Usman ta na cikin matan da suka fi suna a duka Najeriya, ta rike mukamai dabam-dabam a gwamnatocin kasar.

Hadiza Bala Usman ta taba takarar ‘yar majalisa amma ba ta dace ba, a 2015 ta zama shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kaduna.

Hadiza Bala Usman
Hajiya Hadiza Bala Usman ta na da mukami mai girma a mulkin Bola Tinubu Hoto: Hadiza Bala Usman
Asali: Facebook

A lokacin da ta ke rike da wannan matsayi ne aka nada ta a matsayin shugabar hukumar NPA, kujerar da a karshe aka fatattake ta a 2021.

Kara karanta wannan

A ƙarshe, hukumar INEC ta yi magana kan rikicin Majalisar dokokin jihar Ribas

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan sabanin da ta samu da Rotimi Amaechi wanda ya yi shekaru bakwai a matsayin ministan sufuri, ta sake samun babban mukami.

Hadiza ta yi gaba, an manta da Amaechi

Shi kuma Rotimi Amaechi wanda ya nemi tikitin APC domin takarar shugaban kasa bai yi nasara ba, yanzu an daina jin duriyarsa a siyasa.

‘Yar siyasar da ta taka rawar gani a yakin neman zaben Bola Tinubu ta zama hadima a bangaren kula da manufofin gwamnatin tarayya.

Matsayin Hadiza Bala Usman a mulkin Tinubu

A ofishin CDCU da ta ke ciki a yau, Hadiza Bala Usman ta na sa ido a aikin kowane minista domin tabbatar da ya yi abin da ake bukata.

Kwanaki da aka hana Seyi Tinubu halartar taron FEC, Bala Usman ta na cikin wadanda fadar shugaban kasa ta yi wa izinin gani.

Kara karanta wannan

'APC ta shiga uku': An ci gyaran Tinubu kan korar Minista, an fada masa illar hakan

Kamar yadda Punch ta rahoto, Hadiza Usman ta fito da tsari da gwamnati ta ke bi wajen auna kokarin wadanda Tinubu ya ba mukamai.

Daga cikin hanyoyin da ake bi akwai duba kwazon masu mukamai tare da tabbatar da cewa suna kan manufofin Mai girma Bola Tinubu.

An rahoto kwararriyar matar ta kuma ba ‘yan Najeriya damar fadin ra’ayinsu kan ayyukan da ministoci su ke yi, abin da ba a saba ji ba.

Hadimin shugaban kasa kan labarai da dabaru ya taba cewa a game da ita:

"Hadiza ta bullo da wani tsarin fasaha na zamani, inda ta nemi ƴan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu kan ƙoƙarin ministocin."
"A karshe dai sakamakon ya dogara ne da hujjoji masu ma'ana da kuma ra'ayoyin ƴan Najeriya kan nagartar ministocin, ba ruwan Tinubu shi kawai ya aiwatar da abin da jama'a suka yanke."

- Bayo Onanuga.

Garambawul a majalisar ministoci

Ana da labarin Bola Tinubu ya kori wasu ministoci sannan ya sauyawa wasu wurin aiki, ana tunanin da hannun Hadiza Bala a ciki.

Ko da wasu suna ganin an yi son kai wajen korar wasu ministocin, fadar shugaban kasa ta nuna ba da kai Bola Tinubu ya yi aikin ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng