Buhari ya tabbatar da fatattakar Hadiza Bala-Usman daga kujerar Hukumar NPA

Buhari ya tabbatar da fatattakar Hadiza Bala-Usman daga kujerar Hukumar NPA

  • Wani kamfani ya kai karar gwamnati game da dakatar da Hadiza Bala Usman
  • Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da kotu cewa tuni ya kori Bala Usman
  • A baya aka dakatar da shugabar NPA, aka fake da sunan za a binciki hukumar

Mai girma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tabbatar da korar Hadiza Bala-Usman daga hukumar NPA, jaridar Punch ta fitar da wannan rahoto.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana wannan ne a wata a wata takarda da ya gabatar a gaban kotun tarayya a garin Legas a wata shari’a da aka yi.

Rahoton ya bayyana cewa shugaban kamfanin Maritime Media Limited, Asu Beks ya kai karar gwamnatin Buhari a kotu, a kan nadin mukamai a NPA.

KU KARANTA: Ana cigaba da binciken NPA a kan zargin 'badakalar' N132bn

A wannan shari’a mai lamba FHC/L/CS/485/2021, an kalubalanci karfin ikon shugaban kasa na nada shugabanni da darektoci a NPA ba tare da bin doka ba.

Kara karanta wannan

Bayan kame Sunday Igboho, Buhari ya magantu kan masu yunkurin dagula kasa

Har ila yau, wanda suka shigar da karar a kotu su na ikirarin an sallami Hadiza Bala Usman daga aiki a lokacin a saura watanni shida wa’adinta ya kare a ofis.

Shugaban kasar ya maida martani ta hannun wani Lauyan gwamnati mai suna Agan Tabitha, wanda yake aiki a wani sashe a ma’aikatar shari’a ta tarayya.

Agan Tabitha a madadin lauyan shugaba Muhammadu Buhari, ya fada wa kotu cewa Bala-Usman da aka kawo kara a kanta, ta rasa kujerar da ta ke kai a NPA.

KU KARANTA: Ba mu fifita Dangote a NPA ba - Hadiza Bala Usman

Hadiza Bala-Usman
Hadiza Bala Usman Hoto: bizafricadaily.com
Asali: UGC

Tabitha yake fada wa kotu cewa gwamnatin tarayya ta soke nadin mukamin da ta yi wa Bala Usman.

Lauyan ya kalubalanci wannan shari’a, ya ce kamfanin Maritime Media Limited da sauran wadanda suka kawo maganar gaban Alkali, ba su da iko.

Mai kare gwamnatin tarayyar, ya roki Alkali ya yi watsi da wannan shari’a da ke gabansa. Alkali mai shari’a Tjjani Ringim ne yake sauraron shari’ar a Ikoyi.

Kara karanta wannan

Ndume na rokon kotu da ta tsame shi daga shari'ar Maina, ta bashi kadarorinsa

A baya kun ji cewa rikicin cikin gidan da ake yi tsakanin shugabar NPA, Hadiza Bala Usman da Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya dauki wani irin yanayi.

An ce Ministan ya yi watsi da zargin da yake yi wa shugabar ta NPA na kin dawo da Naira biliyan 165 cikin asusu, ya ce Bala-Usman ta na yi masa rashin kunya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel