Sanata Goje Ya Yi Magana, Ya Karyata Zargin da Ake Yi Masa Wajen Bikin Diyarsa

Sanata Goje Ya Yi Magana, Ya Karyata Zargin da Ake Yi Masa Wajen Bikin Diyarsa

  • Tsohon gwamnan jihar Gombe, Sanata Danjuma Goje ya bayyana rashin jin dadin yadda ake zargin watsa kudi a bikin diyarsa
  • An daura auren Fauziyya Danjuma Goje da angonta, Aliyu Ahmed Abubakar a Abuja, shugaba Bola Tinubu ya zama waliyyin amarya
  • A sanarwar da hadimin Sanata Goje ya fitar, ya ce masu yada bidiyon na kokarin bata masa suna duk da ba zai taba karya dokar kasa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Gombe - Tsohon gwamnan Gombe, Sanata Danjuma Goje ya musanta cewa an rika watsa kudi a bikin ‘yar sa, Fauziyya Danjuma Goje da angonta, Aliyu Ahmed Abubakar.

Kara karanta wannan

Gidajen mai wayam, yan Najeriya sun fara hakura da amfani da fetur

Sanata Danjuma Goje shi ne ke wakiltar Gombe ta Tsakiya a majalisar dattawan kasar nan, kuma ya aurar da diyarsa a Juma’ar da ta gabata a Abuja.

Bikin
Sanata Goje ya musanta watsa kudi a bikin diyarsa Hoto: Muhammad Adamu Yayari
Asali: Facebook

A sanarwar da hadimin Sanatan, Muhammad Adamu Yayari ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce ana yada bidiyon watsa kudi a bikin Fauziyya ne domin a batawa iyalan Goje suna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ba a watsa kudi a bikin ba:" Sanata

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Sanata Muhammad Danjuma Goje ya ce sun gano yadda jama'a ke kokarin bata masa suna ta hanyar yada bidiyon yada bikin yarsa ana watsa kudi.

Sanata Goje ya bayyana cewa babu gaskiya cikin yadda jama'a ke kokarin cewa an yi almubazzaranci a bikin diyarsa da ya gudana ranar Juma'a.

Sanata Goje ya musanta karya doka

Tsohon gwamnan, Sanata Muhammad Danjuma Goje ya bayyana cewa babu yadda za a yi a karya dokar kasar nan a bikin diyarsa.

Kara karanta wannan

Matan da za su shiga gwamnatin Bola Tinubu bayan sauyi a majalisar FEC

Ya bayyana haka ne yayin da ake yada cewa an zubar da kudi, lamarin da ya saba dokar kasar nan kamar yadda hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ta nanata.

An cafke 'yar Arewa kan watsa kudi

A baya mun ruwaito cewa jami'an hukumar hana yi wa tattalin hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) sun cafke wata 'yar asalin jihar Gombe bisa zargin wulakanta Naira.

An kama Janty Emmanuel bayan an samu bayanan sirri da suka nuna ta na watsa takardun Naira a wani taron biki da ya gudana a G-Connect, kuma tuni ta amsa laifin da ake zarginta da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.