Yadda Na Kusa da Shi Ya Yi wa Yakubu Gowon Juyin Mulki Yana Kasar Waje a 1975

Yadda Na Kusa da Shi Ya Yi wa Yakubu Gowon Juyin Mulki Yana Kasar Waje a 1975

  • Lokacin da Janar Yakubu Danjuma Gowon ya nemi ya yi shekaru 10 a mulki, sojoji suka hambarar da shi
  • Janar Murtala Mohammed ya karbi iko da Najeriya, shi ma bai wuce watanni shida ya na kan karaga ba
  • Gowon ya ce yana da labarin akwai shirye-shiryen yi masa juyin mulki, amma bai gama yarda da batun ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Lagos - Janar Yakubu Danjuma Gowon ya jagoranci Najeriya na tsawon shekaru tara yana matashi, ya na mulki ne yakin basasa ya barke.

A lokacin Yakubu Danjuma Gowon aka shafe shekaru ana yaki, aka samu wadanda suka nemi su kafa kasar Biyafara daga Najeriya.

Gowon
Janar Yakubu Gowon ya san za a yi juyin mulki a Najeriya a 1975 Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Janar Yakubu Gowon ya yi magana

A wata hira da ya yi da jaridar Daily Trust yayin da ya cika shekaru 90 a duniya, Yakubu Gowon ya yi magana game da batutuwa.

Kara karanta wannan

Ana matsalar lantarki. 'yan Arewa sun dura kan Tinubu, sun ragargaje shi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tattaunar Gowon ta tabo zancen juyin mulkin da abokan aikinsa sojoji su ka yi masa, an zarge shi da cewa bai da niyyar mika mulki.

Menene ya jawo aka kifar da Gowon?

Legit Hausa ta fahimci cewa daga cikin zargin da ake yi wa gwamnatin Gowon akwai daurewa marasa gaskiya gindi a mulki.

Bayan kin mika mulki, Gowon ya bar gwamnonin jihohinsa sun dade ba tare da canji ba duk da ana zarginsu da sata da cin amana.

Janar Gowon ya san za a yi juyin mulki?

Gowon ya ce ya ji kishin-kishin za a yi masa juyin mulki, kuma aka zargi shugaban sojojin da ke gadin fadarsa, Kanal Joe N. Garba.

An nunawa Gowon cewa gwamnansa, Tony Ochefu shi ma 'dan asalin Benuwai-Filato yana cikin masu kokarin hambarar da shi.

"Bayanan tsaro sun shaida mani makamancin hakan zai iya faruwa. Sunayen da aka iya ba ni su ne mutanen kusa da ni.

Kara karanta wannan

Masoyan Peter Obi sun yi masa watsa watsa a fili a dalilin turawa Gowon sako

"Dole in zargi sunayen da aka ba ni. Daga jiha ta suke kuma kiristoci ne. Saboda haka ban yarda da zancen dari bisa dari ba."

Gowon ya tunkari Kanal Joe Garba

Da Janar Gowon ya tuntubi Garba, sai ya rantse masa da Ubangiji cewa bai da hannu, ba a dade ba kuwa sojoji suka canza gwamnati.

Da aka kifar da gwamnatin Gowon ya na taro a kasar Uganda a 1975, shugaba Idi Amin ne ya tabbatar masa da labaran da yake ji.

Washegari ya yi jawabi, ya na mai kira da a ba gwamnatin Murtala Mohammed hadin-kai, a 1976 ne aka kashe sabon shugaban.

Peter Obi ya taya Gowon murnar cika shekara 90

An ji labarin yadda Janar Yakubu Gowon ya jawo Peter Obi ya ji babu dadi da ya shiga hannun masoyansa lokacin da ya cika shekara 90.

Yakubu Gowon ya ja daga da Chukwuemeka Ojukwu ya nemi ya raba Najeriya saboda haka har yau ba mutanen Ibo ba su manta da shi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng