Yadda Ake Muzgunawa Musulmi a Turai duk da Ikirarin Sanin Hakkin Dan Adam

Yadda Ake Muzgunawa Musulmi a Turai duk da Ikirarin Sanin Hakkin Dan Adam

  • An samu karuwar cin zarafin Musulmai da ke zaune a sassa daban-daban na kasashen Turawan yamma
  • Alkaluman da shirin 'kasancewa musulmi a tarayyar Turai' ya tattaro a 2022 ya nuna yadda ake cin zarafin Musulmai
  • Alkaluman sun kuma nuna karuwar wariyar launin fata da kin jinin addini ga Musulmai da Musulunci a kasashen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Europe - Bincike ya tabbatar da cewa an samu karuwar cin zarafin Musulmai a fadin Tarayyar Turai.

Alkaluma da hukumar tarayyar Turai kan kare hakkin dan Adam ta tattaro ya nuna cewa ana kyamar fiye da rabin musulmin da ke nahiyar.

Kara karanta wannan

2025: Abba ya sanar da cigaba da daukar daliban Kano zuwa ƙasashen waje

Musulmi
An samu karuwar cin zarafin musulmi Hoto Samuel Kubani
Asali: Getty Images

Kafar RFI ta wallafa yadda aka binciko cewa akalla 47% na musulman da ke zaune a kasashen Turai guda biyar na fuskantar kalubale wariya a ɓangarorin aikin yi da mallakar gidaje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An samu karuwar nuna tsana ga Musulmai

Hukumar kare hakkin dan Adam ta tarayyar Turai ta gudanar da bincike kan Musulmai 9,600 da ke zaune a kasashen nahiyar 13 tsakanin Oktoba 2021 zuwa Oktoba 2022.

Kafar Anadolu Ajansi ta ruwaito daraktar hukumar, Sirpa Rautio ta ce kin jinin Musulmai ya karu, kuma ta danganta haka da harin da Isra'ila ta fara kai wa Gaza a bara.

Kasashen da aka fi tsanar musulmai

Kasar Austria na nuna kyamar sosai ga Musulman da ke zaune a kasar inda aka samu 71%, sai kasar Jamus da ke biye mata da 68%.

Kasar Finland ce ta uku a jerin kasashen da ke nuna kin jinin Musulmai da 63%, kasar Faransa ta na take mata baya da 39% na yawan cin zarafin Musulmi.

Kara karanta wannan

Ana kukan lantarki, ruwa ya karya gadar da ta haɗa ƙauyuka sama da 50

An rufe makarantu kan cin zarafin Musulmi

A wani labarin kun ji cewa mahukunta sun garkame wata makaranta a Indiya biyo bayan cin zarafin daya cikin cikin dalibanta Musulmi ta hanyar sharara masa mari.

An hango wata malama yar addinin Hindu ta tsayar da yaro Musulmi dan shekara bakwai inda ta umarci sauran ɗalibai su rika zuwa su na tsinka masa mari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.