Anci zarafin addinin Musulunci a wakar Shaku Shaku – MURIC

Anci zarafin addinin Musulunci a wakar Shaku Shaku – MURIC

Kungiyar kare hakkin musulmi ta MURIC ta yi Allah wadai da wannan sabon faifon biyon waka na wani mawakin Turanci mai suna Folarin Falana ko inkiya (Falz the Bahd Guy) ya yi.

A cewar kungiyar wakar ya yi tozarci tare da cin mutuncin addinin Musulunci da Musulmi.

Hakazalika kungiyar ta bukaci ayi gaggawar janye wakar daga kasuwa idan har ana son zaman lafiya a kasar.

Wakar it ace wacce aka yiwa lakabi da suna “This is Nigeria” ma’ana “Wannan ita ce Najeriya” inda a cikin wakar aka dinga wata rawa ta rashin mutunci da aka sanya sunan shaku shaku.

Anci zarafin addinin Musulunci a wakar Shaku Shaku – MURIC
Anci zarafin addinin Musulunci a wakar Shaku Shaku – MURIC

A cikin bidiyon wakar an nuna wani Bafulatani yana sare kan mutane babu gaira babu dalili, abinda yake nuna cin zarafi ga kabilar Fulani a Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Ya kamata yan Najeriya su nemi sanin kudaden da ake kashewa Gwamnoni da shugaban kasa – Shehu Sani

Sannan kuma a cikin akar an ci zarafin addinin Musulunci, inda aka nuna wata mata sanye da Hijabi tana rawar ‘yan kwaya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng