Dan Majalisa a Kano Zai Tura Ƴaƴan Talakawa Karatu Kasar Waje, Bayanai Sun Fito

Dan Majalisa a Kano Zai Tura Ƴaƴan Talakawa Karatu Kasar Waje, Bayanai Sun Fito

  • Dalibai 21 sun samu tallafin zuwa yin karatu a Jami'ar Fasaha ta Malaysia (UTM), za su shafe watanni 18 suna karatu a can
  • Dan majalisa mai wakiltar mazabar Bichi daga jihar Kano, Hon. Abubakar Kabir Bichi ne ya dauki nauyin karatun daliban
  • Bichi ya bayyana cewa ya cika alkawarin da ya daukarwa 'yan mazabarsa na ba su tallafin karatu ba tare da wariya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Dan majalisa mai wakiltar mazabar Bichi daga jihar Kano, Hon. Abubakar Kabir Bichi ya dauki nauyin karatun daliban mazabarsa 21.

Hon. Abubakar Bichi ya dauki nauyin daliban su je su yi karatu a kasar Malaysia karkashin shirin tallafin karatun da ya ke bai wa 'yan mazabarsa.

Kara karanta wannan

Kaico: Ɗalibai 2 sun mutu a wani harin kwantan ɓauna, mutane sun shiga jimami

Dan majalisar wakilai a Kano ya yi magana kan tura dalibai karatu kasar waje
Dan majalisar wakilai na Bichi, ya tura dalibai 21 karatu zuwa Malaysia. Hoto: Hon. Abubakar Kabiru Abubakar Bichi
Asali: Facebook

Dan majalisa ya tura dalibai Malaysia

Wadanda suka ci gajiyar tallafin za su yi karatu na tsawon watanni 18 a fannin Injiniyanci, kimiyyar kwamfuta, fasaha da dai sauran darussa, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce daliban 21 da suka samu wannan dama, za su yi karatu ne a Jami'ar Fasaha ta Malaysia (UTM), ɗaya daga cikin manyan jami'o'i a Malaysia.

An gabatar da takardun guraben karatu da sauran kayayyakin bukata ga dukkanin daliban 21 a karamar hukumar Bichi a ranar Laraba.

Kano: Dan majalisa ya gwangwaje dalibai

Haka kuma dan majalisar wakilan ya dauki nauyin dalibai 59 domin su yi karatu a babbar sakandare (SS1 zuwa SS3) a bangaren kimiyya da fasaha tare da ba su kayan karatu.

Hon. Abubakar Bichi ya kuma dauki malaman boko 150 da na Islamiyya 50 domin su koyar a makarantu daban-daban na karamar hukumar, tare da karin albashi ga malamai 106.

Kara karanta wannan

2025: Abba ya sanar da cigaba da daukar daliban Kano zuwa ƙasashen waje

Da yake jaddada cika alkawarin da ya daukarwa al'ummar Bichi shekaru biyu da suka wuce, dan majalisar ya ce:

“An zabo daliban da suka ci gajiyar tallafin ne bisa cancanta kuma babu wani dan uwana a cikinsu. Sun tsallake matakan tantancewa mai tsanani. Ban taba ko ganinsu ba."

Abba zai tura karin dalibai kasar waje

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna Abba Yusuf ya yi wa daliban Kano albishir na shirin sake tura hazikan daliban jihar zuwa karatu kasashen ketare.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta tura dalibai 1001 zuwa ketare da wasu jami'o'in Najeriya a zango na 2024/2025 domin zurfafa karatu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.