'Yan Najeriya Su Shirya: Majalisa Ta ba CBN Sabon Umarnin Janye Tsofaffin Naira

'Yan Najeriya Su Shirya: Majalisa Ta ba CBN Sabon Umarnin Janye Tsofaffin Naira

  • Majalisar wakilai ta ba babban bankin Najeriya (CBN) sabon umarni na fara janye tsofaffin takardun Naira daga hannun jama'a
  • Bayan wani kudurin gaggawa da Hon. Adam Victor Ogene ya gabatar, majalisar ta umarci CBN ya wadatar da sababbin kudi a kasar
  • Hon. Ogene ya nuna damuwa kan halin da 'yan kasar za su shiga idan wa'adin daina amfani da tsofaffin kudin ya kare a Disamba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Majalisar wakilai ta bukaci babban bankin Najeriya (CBN) da ya wadatar da sababbin takardun kudi na N200, N500 da N1,000 a fadin kasar nan.

Hakazalika, majalisar ta bukaci CBN da ya fara janye tsofaffin Naira daga hannun jama'a ta yadda sababbin kawai za su rika yawo.

Kara karanta wannan

Duk da Dala ta haura N1600, IMF ya yabi kokarin CBN, ya yi ikirarin Naira ta mike

CBN: Majalisar wakilai ta yi magana game da janye takardun Naira daga hannun jama'a
Majalisar wakilai ta umarci CBN ta fara janye tsofaffin takardun Naira. Hoto: Bloomberg/contributor
Asali: Getty Images

Majalisa ta bukaci a saki sababbin kudi

Majalisar ta dauki matakin ne biyo bayan wani kudirin gaggawa na mahimmanci ga jama'a da Hon. Adam Victor Ogene (LP, Anambra) ya gabatar, inji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce majalisar ta bukaci CBN da ya umarci bankuna su fitar da sabbin takardun kudi ga kwastomomi da kuma yin aikin janye tsofaffin kudin.

Majalisar ta kuma ce ya kamata babban bankin ya fara wayar da kan ‘yan Najeriya game da wa’adin ranar 31 ga Disamba, 2024 na daina amfani da tsofaffin kudin.

Dan majalisa na korafi kan shirun CBN

Da yake jagorantar muhawara kan kudirin, Hon. Ogene ya tuno da ce-ce-ku-ce da wahalhalun da aka shiga a kasare bayan CBN ya canja takardun Naira a 2023.

Ya kuma tuno da yadda karancin takardun kudin ya haifar da tsadar rayuwa da kunci ga al’umma sakamakon gazawar CBN na samar da sabbin takardun kudin.

Kara karanta wannan

Tattalin arziki: Gwamnati ta fadi yadda za a hana Dala tashi kan Naira

Hon. Ogene ya nuna takaici na yadda CBN ta yi shiru ba tare da fara wani shiri na wayar da kan jama'a game da wa'adin daina amfani da tsofaffin kudin a karshen 2024 ba.

Ya ce ‘yan Najeriya na iya shiga cikin mawuyacin hali fiye da wanda suka shiga a watan Fabrairu, 2023 idan wa'adin amfani da tsofaffin takardun kudin ya kare.

Kotu ta yi hukunci kan tsofaffin Naira

A wani labarin, mun ruwaito cewa Kotun Koli ta yanke hukuncin cewa 'yan Najeriya su ci gaba da amfani da sababbi da tsofaffin takardun Naira har sai baba-ta-gani.

Da yake zartar da hukuncin, kwamitin alkalai bakwai karkashin jagorancin Inyang Okoro, ya ce za a ci gaba da amfani tsofaffi da sababbin N200, N500 da N1000.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.