Tattalin Arziki: Gwamnati Ta Fadi Yadda za a Hana Dala Tashi kan Naira
- Ministan tattalin arziki, Wale Edun ya yi magana kan yadda kudin waje ke cigaba da haurawa kan Naira a kasuwar canji
- An ruwaito cewaEdun ya yi bayani ne yayin wani taro a birnin Washington DC na kasar Amurka da bankin duniya da IMF suka shirya
- Ministan kuɗin ya fadi hanyar da za a bi a Najeriya wajen ganin darajar Naira ba ta cigaba da yin kasa ba a kasuwar canji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ministan kudin Najeriya, Wale Edun ya koka kan yadda darajar Naira ke cigaba da faduwa a duniya.
Wale Edun ya bayyana matakin da za a dauka a gwamnatance domin farfaɗo da darajar Naira a fadin duniya.
Premium Times ta wallafa cewa tun a watan Fabrairu bankin CBN ke nuna fargabar cigaba da tashin Dala a kan Naira.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Minista ya koka da tashin Dala kan Naira
Ministan kudi, Wale Edun ya nuna damuwa kan yadda ake cigaba da samun tashin Dala a kan Naira.
Wale Edun ya ce daga cikin abubuwan da suke kawo tashin Dala akwai tsarin da ake bi wajen rarraba harajin FAAC ga jihohi da kananan hukumomi.
Yadda za a hana Dala tashi a Najeriya
Yayin tattaunawa da yan jarida, Wale Edun ya bayyana cewa Najeriya kasa ce mai arzikin man fetur da ake sayarwa a kasashen duniya.
Business Day ta wallafa cewa ministan ya ce idan Najeriya ta kara adadin man fetur da take hakowa za ta magance matsalar tashin Dala.
"Idan mu ka kara adadin albarkatun man fetur da muke hakowa za mu huta da bukatar dala sosai wanda hakan zai rage mata farashi"
-Wale Edun
Taron tattalin arziki a kasar Amurka
Ministan kuɗin Najeriya, Wale Edun ya je Amurka ne domin taron kasashe masu tasowa na G-24 saboda tattauna lamuran tattali.
Ministoci da gwamnonin kasashen G-24 da jami'an gwamnati ne suka halarci taron wannar shekarar da aka yi a birnin Washington DC.
Za a tura kudi ga talakawa ta banki
A wani rahoton, kun ji cewa ministan kudin Najeriya, Wale Edun ya ce gwamnatin tarayya za ta tura kuɗi ga talakawan kasar nan ta asusun banki.
Wale Edun ya bayyana cewa akalla talakawa miliyan 20 ne za a turawa kudi ta asusun banki domin rage radadin rayuwa a kasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng