'Ya Ƙware': Yadda Ɗan Shekara 17 Ya Yi Kutse a Na'urar Shugaban Hukumar EFCC
- Wani yaro dan shekara 17 ya gigita shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede da irin kaifin basirar da yake da ita a sarrafa nau'ura
- Olukoyede ya ce yaron ya yi kutse a cikin na'urarsa (kwamfuta) a gabansa ba tare da ya ba shi wasu lambobin sirri na bude ta ba
- Shugaban EFCC ya ce akwai bukatar al'ummar kasar su canja tunani a wajen tunkarar matsalolin aikata laifuffuka a yanar gizo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya tuno ganawarsa da wani yaro dan shekara 17 da ake zargi da aikata laifuffukan yanar gizo.
Mista Olukoyede ya ce yaron, wanda bai bayyana sunansa ba, ya nuna kwarewa a sarrafa na'ura mai kwakwalwa wanda har ya sanya shi kaduwa.
Shugaban EFCC ya hadu da 'dan baiwa'
Shugaban EFCC ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wajen taron kaddamar da cibiyar yaki da laifuffukan yanar gizo a Abuja inji rahoton Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce lamarin yaron ya nuna bukatar samun canji daga al’umma wajen tunkarar matsalolin da ke tattare da aikata laifuffuka ta yanar gizo.
Mista Olukyede ya ce ya yanke shawarar gwada yaron; dalibin jami'a a shekara ta farko da ke karatun tarihi, domin ya ga "irin bajinta da kwarewarsa."
Dan shekara 17 ya yi wa Olukoyede kutse
A labarin fikirar yaron da ya bayar, shugaban EFCC ya ce:
"Na ba shi na'ura ta (komfuta). 'Ta ya ka iya yin hakan?' Kuma fa abin mamakin karatun tarihi ya ke yi ba wai kimiyya ba. Amma sai ka ga irin basirarsa.
"Ya bude na'urata ba tare da na ba sa lambobin sirrin bude ta ba, shi da kansa ya gano. Ni dai na tsaya ina kallon ikon Allah, cikin mamaki.
"Amma wannan ba abin wasa ba ne, Hakan na nufin muna da masu kaifin basira a Najeriya. Har kokarin yin kutse a asusun banki na ya so yi, amma na dakatar da shi."
Gwamoni 2 sun gayyato hukumar EFCC
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda da takwaransa na Ekiti, Biodun Oyebanji sun gayyato hukumar EFCC jihohinsu.
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede ya ce hukumar yanzu ta samu kyautar kadarorin da za ta yi amfani da su a matsayin ofishi a jihohin Katsina da Ekiti.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng