EFCC ta kama yan gida daya su hudu da wasu uku kan damfarar yanar gizo

EFCC ta kama yan gida daya su hudu da wasu uku kan damfarar yanar gizo

- Hukumar EFCC reshen Ibadan ta kama wasu matasa bakwai kan damfara ta intanet

- Kayayyakin da aka samo daga yan damfarar sun hada da motoci hudu, kwamfutocin Laptop, da kuma manyan wayoyi

- Hukumar yaki da rashawar ta ce za a mika wadanda ake zargin kotu da zaran an kammala bincike

Hukumar yaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ta kama wasu yan gida daya su hudu da wasu matasa uku kan damfarar intanet a Ibadan, jihar Oyo.

A bisa ga wani jawabi da aka wallafa a shafin EFCC na Twitter a ranar Laraba, 9 ga watan Satumba, yan gida dayan sune; Ayoola Timilehin da Olusola Timilehin, sai kuma Oladayo Fayemi da Tolulope Fayemi.

An kama su ne a mabuyarsu da ke Alaka, yankin Elebu na Ibadan.

EFCC ta kama yan gida daya su hudu da wasu uku kan damfarar yanar gizo
EFCC ta kama yan gida daya su hudu da wasu uku kan damfarar yanar gizo Hoto: EFCC
Asali: Twitter

Sauran ukun da aka kama sune Temitope Kumuyi, Babatunde Oyelakin da Olanrewaju Ibrahim. Duk suna tsakanin shekaru 20 da 30 ne.

KU KARANTA KUMA: Zan dauki kaddara idan na sha kaye a zabe na gaskiya - Obaseki

Kayayyakin da aka samo daga hannunsu sun hada da motoci hudu, kwamfutocin laptop, manyan wayoyi da kuma wani hatimi da ke dauke da sunan ofishin kula da kudi na jami'ar koyon aikin likitanci ta Queensland da ke Australia.

Hukumar ta bayyana cewa an kama su ne sakamakon bayanan sirri da aka samu kansu cewa suna rayuwa ta kasaita ba tare da an san hanyar samun kudinsu ba.

Jawabin ya kuma bayyana cewa za a mika wadanda ake zargin kotu da zaran an kammala bincike.

A wani labarin kuma, an cafke wasu dalibai hudu 'yan Nigeria a birnin Muntinlupa, kasar Philippine bisa zarginsu da laifin yin kutse a na'urar bankunan kasar tare da sace kudade.

KU KARANTA KUMA: Rashawa: Gwamna Sule zai yi sauye-sauye a majalisar zartarwa ta jihar Nasarawa

Sai dai, gaba daya 'yan Nigerian hudu, sun musanya wannan zargi da ake yi masu. Hukumar binciken kudade ta kasar ta sanar da hakan a ranar Talata.

Sanarwar na dauke da sa hannun shugaban sashen binciken laifukan kutse ta yanar gizo na hukumar NBI, Vic Lorenzo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel