An gano wata babbar barazanar kutse ta yanar gizo a Najeriya

An gano wata babbar barazanar kutse ta yanar gizo a Najeriya

- Masu kutse na shirin satar bayanai a Najeriya

- Sanarwar ta fito daga hukumar bunkasa bayyanan kimiyar sadarwa ta Najeriya

- Hukumar ta bayyana cewar masu kutsen suna shirin kawo farmakin ne a kasar, musamman ma akan bankuna da wasu ma'aikatun gwamnati

An gano wata babbar barazanar kutse ta yanar gizo a Najeriya
An gano wata babbar barazanar kutse ta yanar gizo a Najeriya

Sanarwar da hukumar bunkasa bayyanan kimiyar sadarwa ta fitar kan barazanar kai wa Najeriya hari ta yanar gizo ya sa majalisar dattawan kasar tsayar da kudurori biyu domin kare kasar daga duk wata barazanar sace bayyanai ta yanar gizo ko yada labaran karya.

An ankarar da Najeriya akan hari ta yanar gizo da za'a iya kai wa naurori masu kwakwalwa cikin kasar, musamman ma akan bankuna da wasu ma'aikatun gwamnati.

DUBA WANNAN: Bankunan Najeriya zasu fara aiki da fasahar CRS

Hukumar bunkasa bayanan kimiyar sadarwa ce ta fitar da sanarwa da ta bayyana kalubalen a fili.

Hukumar ta ce masu satar bayanai na shirin kawo farmaki kan kafofin sadarwan Najeriya.

A cewar hukumar hakan ya zama wajibi kafofin gwamnati da kamfanoni da masu zaman kansu su samar da garkuwa daga wannan barazanar.

Yin hakan ya hada da kaucewa yanar gizo ta kyauta idan ba ya zama dole ba.

Kaucewa musayar hotuna ko aikawa da sako tsakanin wayoyin salula ta manhajar Bluetooth barkatai da sanya garkuwar yaki da abubuwa da kan illarta na'urori masu kwakwalwa ta hanyar yanar gizo.

Maganar ta kai zauren Majalisar Dattawan Najeriya inda aka zanta akan lamarin.

Wannan lamari ya sa, Majalisar Dattawa ta gudanar da muhawara kan wannan barazana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng