'A kan Titi Muke Kwana': Wata Zanga Zanga Ta Barke a Sokoto saboda Shirin Rusa Gidaje
- Gomman mutane maza da mata ne suka kaddamar da zanga zangar adawa da gwamnatin jihar Sokoto a ranar Talata, 22 ga Oktoba
- Masu zanga zangar sun zargi gwamnatin Sokoto da korarsu daga gidajen da suka shafe shekara da shekaru suna rayuwa a ciki
- An rahoto cewa gwamnati ta kori mazauna rukunin gidaje na Yauri Plats a makon jiya, lamarin da ya tilastawa wasu kwana a titi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sokoto - Mazauna rukunin gidaje na Yauri Plats da ke Sokoto sun gudanar da zanga zangar lumana domin nuna adawa da matakin gwamnatin jihar.
An ga gomman mazauna Yauri Plats a ranar Talata suna zanga zanga kan korarsu daga rukunin gidajen da gwamnatin jihar ta yi.
Masu zanga-zangar, sun mamaye sakatariyar kungiyar 'yan jarida ta Najeriya dauke da kwalaye da rubuce-rubuce daban-daban inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Sokoto za ta rusa Yauri Plats
Masu zanga-zangar dai sun yi zargin cewa korarsu daga gidajen da suka shafe sama da shekaru 40 suna zama a ciki ba daidai ba ne.
An tattaro cewa akalla dakuna 180 kowanne mai dauke da akalla mutane shida ne gwamnatin jihar Sokoto ta sanyawa alamar rusawa a rukunin gidaje na Yauri Plats.
Mazauna gidajen da abin ya shafa da suka hada da mata da yara na kwana a filin Allah kusa da rukunin gidajen tun bayan korar da aka yi musu a makon jiya.
Sun yi ikirarin cewa gwamnatin jihar Sokoto ba ta biya diyya ba, kuma ba ta ba su wani wurin kwana kafin a kore su ba.
'A titi yanzu muke kwana' - Mazauna
Talatu Yusuf, daya daga cikin mutanen da aka haifa kuma suka girma a rukunin gidajen, ta shaida wa Aminiya cewa tun a 1992 iyayenta ke zama a gidan.
“An kore mu a makon da ya gabata kuma a halin yanzu, ba mu da wani matsugunni. Tun makon da ya gabata muke kwana a filin Allah.”
- A cewar Talatu.
Wata mata mai suna Malama Aisha Bala ta ce ta shafe shekara 21 a gidan da take ciki, ta ce an tilasta musu kwana a kan titi bayan korar su.
Zanga zanga ta barke a Sokoto
A wani labarin, mun ruwaito cewa fusatattun mutane sun gudanar da zanga-zanga kan nisan da 'yan bindiga suka yi wa Sarkin Gobir, Alhaji Isa Muhammad Bawa a jihar Sokoto.
A yayin zanga-zanga a garin Sabon Birni, an ce an yi kone-kone a kan tituna domin nuna adawa da kisan gillar da 'yan bindigan suka yiwa basaraken.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng