'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Sansanin 'Yan Sanda a Katsina, An Rasa Rayuka
- Wasu gungun 'yan bindiga sun kashe jami'an 'yan sanda hudu da fararen hula biyu a wani sabon hari da suka kai jihar Katsina
- An rahoto cewa 'yan bindigar sun farmaki sansanin da jami'an tsaron ke zama a garin Garagi, kauyen Yartsamiyar Jino
- Mazauna yankin da suka zanta da manema labarai sun ce 'yan ta'addan sun yi awon gaba da bindigogin 'yan sandan da aka kashe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - 'Yan bindiga sun kai hari sansanin ‘yan sandan Mopol da ke Garagi a kauyen Yartsamiyar Jino da ke a jihar Katsina.
An ce 'yan bindigar sun farmaki sansanin 'yan sandan da ke a karamar hukumar Kankara a ranar Talata, 22 ga watan Oktobar 2024.
'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda
A cewar wani rahoto na jaridar Daily Trust, mazauna yankin sun ce harin ya yi sanadin mutuwar jami’an tsaro hudu, yayin da jami’i daya ya samu raunuka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun kara da cewa maharan sun kuma kwashe bindigogin jami’an da suka kashe a lokacin da lamarin ya faru.
Baya ga asarar rayuka da jami’an tsaro suka yi, maharan sun kuma kashe wasu fararen hula biyu daga cikin yankin.
Hari kan sansanin 'yan sandan Katsina
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce maharan sun kai hari ne a makarantar firamare da ke Tsamiyar Jino.
A cewarsa, jami'an tsaron na sun dade suna amfani da ajujuwan makarantar a matsayin sansaninsu, wanda ya sa aka farmaki makarantar.
Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Katsina: 'Yan bindiga sun farmaki sojoji
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu gungun 'yan bindiga sun farmaki sansanin sojojin da aka girke a kauyen kauyen Nahutu da ke karamar hukumar Batsari, jihar Katsina.
A yayin da wani bangare ke farmakar sojojin, an ce wani bangare na 'yan ta'addan sun kutsa kauyen Nahutu, suka fasa shaguna da gidaje tare da sace kayayyaki da dabbobi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng