Rabiu Kwankwaso Ya ba Gwamnati Kyautar Wata Sabuwar Makaranta da Ya Gina

Rabiu Kwankwaso Ya ba Gwamnati Kyautar Wata Sabuwar Makaranta da Ya Gina

  • Jagoran jam'iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ba da kyautar sabuwar makaranta ga gwamnatin Kano
  • An rahoto cewa Kwankwaso ya gina makarantar mai ajujuwa tara a garin Rikadawa a karamar hukumar Madobi da ke Kano
  • Wannan na zuwa ne yayin da tsohon dan takarar shugaban kasar kuma tsohon gwamnan na Kano ya ke bikin cika shekaru 68

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ya ba ma'aikatar ilimi ta jihar Kano kyautar sabuwar makaranta da ya gina.

An ce Rabiu Kwankwaso ya bayar da kyautar makarantar ne a matsayin wani bangare na bikin murnar cikarsa shekaru 68 a duniya.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya fadi kokarin da ya yi da yake mulki, ya koka da rashin tsaro a yau

Gwamnatin Kano ta yi magana yayin da Kwankwaso ya ba ta kyautar sabuwar makaranta
Sanata Rabiu Kwankwaso ya gwangwaje gwamnatin Kano da kyautar sabuwar makaranta. Hoto: Auwalu Musa Yola
Asali: Facebook

Jami'in watsa labarai na karamar hukumar Madobi, Auwalu Musa Yola ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook a ranar Litinin, 21 ga Oktoba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rabiu Kwankwaso ya ba da kyautar makaranta

Sanarwar da Auwalu Musa Yola ya fitar ta bayyana cewa:

"Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya ba da kyautar makaranta mai dauke da ajujuwa tara a gundumar Rikadawa, karamar hukumar Madobi ga ma'aikatar ilimi ta jihar Kano.
"Ba da kyautar makarantar karamar sakandare ta addini ga gwamnati na daga cikin murnar da ya ke yi na bikin cika shekaru 68."

Sanarwar ta ce wannan yunkuri da Kwankwaso ya yi ya kara fito da fifikonsa ga ilimi, kuma hujja ce ga kokarin da ya yi na gina jami'ar KUST Wudil da NWU lokacin da ya ke gwamna.

Gwamnati ta jinjinawa Sanata Kwankwaso

Kara karanta wannan

Rikicin APC ya ƙara ƙamari, babban basarake a Arewa ya yi murabus daga sarauta

Yunkurin da Kwankwaso ya yi a fannin ilimi a baya ya haifar da karuwar masu shiga makarantu, inda ya nuna kwazonsa na karfafa guiwar yara, a cewar sanarwar.

Da ya ke karbar makarantar a madadin gwamnatin Kano, kwamishinan ilimi, Dakta Umar Haruna Doguwa ya tabbatar da bunkasar tsarin ilimi a jihar

Sanarwar ta ruwaito kwamishinan na cewa:

"Irin wadannan ayyukan ne ke karawa Kwankwaso kwarjini da kara tabbatar da matsayinsa na mai fafutukar ganin yara sun samu ilimi da kuma ci gaban al’umma Kano."

Abba ya aika sako ga Kwankwaso

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya turawa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso sakon taya shi murnar cika shekaru 68 da haihuwa.

Gwamna Abba ya ce ya san Rabi'u Kwankwaso a matsayin mutum mai gaskiya, jarumi kuma mai taimakon jama'a a iya shekaru 38 da ya kasance yana aiki tare da shi.

Kara karanta wannan

Direbobin da ke bin babbar hanya a Arewa za su fara biyan haraji a sabon tsari

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.