Kwankwaso ya gina makarantar makiyaya don murnar cika shekaru 64 a duniya

Kwankwaso ya gina makarantar makiyaya don murnar cika shekaru 64 a duniya

- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na jihar Kano ya gina makarantar makiyaya

- Kwankwaso ya yi hakan ne daga cikin tsare-tsaren murnar cikarsa shekaru 64 a duniya

- An kaddamar da makarantar ne a garin Munture da ke karamar hukumar Rano da ke jihar Kano domin yaran makiyaya da ke yankin

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a ranar Talata, 20 ga watan Oktoba, ya kaddamar da wata makarantar makiyaya a garin Munture da ke karamar hukumar Rano da ke jihar.

Kaddamar da ginin na daga cikin jerin abubuwan da aka tsara gudanarwa domin bikin cikarsa shekaru 64 a duniya, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Makarantar wacce gidauniyar Kwankwasiyya ta gina kuma ta kunshi sassa uku da ajujuwa shida zai dauki dalibai makiyaya akalla guda 300 a yankin.

KU KARANTA KUMA: An kama mutane hudu da ake zargi da kai wa kwamandan yan sanda hari

Kwankwaso ya gina makarantar makiyaya don murnar cika shekaru 64 da haihuwarsa
Kwankwaso ya gina makarantar makiyaya don murnar cika shekaru 64 da haihuwarsa Hoto: @BBCHausa
Asali: Twitter

Da yake jawabi a yayin kaddamar da ginin, Sanata Kwankwaso ya ce ya yanke shawarar daga darajar makaratar, wacce take Islamiyya zalla a baya domin samar da ilimi ga yaran.

Kwankwaso wanda ya kuma kasance tsohon sanata da ya wakilcin Kano ta tsakiya a Majalisar Dattawa ta takwas, ya ce yana da burin ganin ya tallafawa ilimin yaran yankin har zuwa matakin jami’a.

A cewarsa, “Babban buri na shine na ga na samarwa da al’umma ilimi, musamman ma ‘ya’yan talakawa saboda ta hanyar ilimantar da jama’a ne kawai za ka iya ceto su daga duhun kai, wannan kuma ita ce akidar tafiyarmu.

KU KARANTA KUMA: An yi arangama tsakanin ƴan sanda ta ɓata gari a Lagos, mutane 2 sun mutu

“Wannan makaranta ta jima sosai amma a matsayin ta Islamiyya zallah. Sai muka ga ya dace mu gina musu ita domin ta bayar da ilimin boko da na Islamiyya,” inji shi.

Ya yi kira ga al’ummar yankin da su yi amfani da makarantar yadda ya kamata ta hanyar tura yaransu cikinta da kuma kula da ita domin amfanin yankin gaba daya.

A gefe guda, mun ji cewa Kwankwaso, ya kafa gidan rediyo a jihar Kano kuma ya nada tsohon dan jaridar BBC, Maude Gwadabe a matsayin manajan farko.

Gidan rediyon mai suna Nasara Rediyo, ya samun amincewar hukumar yada labarai ta kasa NBC, da su fara watsa labarai a kan 98.5 FM, Daily Nigerian ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng