Zanga Zangar Tunawa da Ranar ENDSARS Ta Barke, 'Yan Sanda Sun Dauki Mataki

Zanga Zangar Tunawa da Ranar ENDSARS Ta Barke, 'Yan Sanda Sun Dauki Mataki

  • Masu zanga-zanga sun mamaye Lekki Toll Gate da ke Legas domin tunawa da ranar da aka yi zanga-zangar EndSARS karo na 4
  • An ce sun yi taron ne domin sake nuna takaicin su kan zaluncin ‘yan sanda da kuma kashe matasan da aka yi shekaru hudu baya
  • To sai dai kuma zanga zangar ta dauki salo bayan jami’an ‘yan sanda sun harba barkonon tsohuwa tare da cafke masu gangamin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Jami’an ‘yan sandan Najeriya sun kama wasu daga cikin masu zanga-zangar da suka yi dandazo a kan titin Lekki a jihar Legas.

Masu zanga-zangar sun taru ne a ranar yau Lahadi domin tunawa da 'zaluncin' da suka ce jami'an tsaro sun yi wanda ya yi ajalin matasa a ranar 20 ga Oktoba, 2020.

Kara karanta wannan

Satar wayoyi 100 ta jefa wasu daliban Arewa a cikin matsala, 'yan sanda sun yi bayani

'Yan sanda sun cafke masu zanga zangar tunawa da ranar ENDSARS a Legas
Legas: 'Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa tare da cafke masu zanga zangar ENDSARS
Asali: Getty Images

ENDSARS: An kashe matasa 12

Matasan da suka yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da zaluncin ‘yan sanda sun yi kira da a rusa sashen ‘yan sanda na SARS inji rahoton Dailty Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bisa wannan bukata, hukumomin ‘yan sanda sun rusa SARS amma masu zanga-zangar sun barin kan tituna, musamman ma a Tollgate din da ya zamo dabdalar matasan.

Gwamna Babajide Sanwo-Olu dai ya ayyana dokar ta-baci, amma masu zanga-zangar sun ki sauka daga babbar kofar karbar harajin, lamarin da ya sa aka tura sojoji.

Sojojin sun bude wuta, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane, kamar yadda shaidu suka bayyana, amma hukumomin sojin da gwamnatin tarayya sun musanta kisan.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta ce an kashe masu zanga-zangar 12 a lokacin da sojoji suka shiga tsakani.

Kara karanta wannan

CNG: Ana jimamin hatsarin Jigawa, mota mai amfani da gas ta fashe a gidan mai

EndSARS: An kama masu zanga-zanga

A safiyar Lahadi, 20 ga Oktobar 2024 ne dai aka cika shekaru 4 da aukuwar lamarin, wasu masu zanga-zangar sun taru a bakin Lekki tollgate, suna wake-wake tare da daga alluna.

Sai dai ‘yan sandan da ke kasa sun yi kokarin tarwatsa su da barkonon tsohuwa da kuma harbin bindiga a saman iska, inji rahoton Punch.

Ana cikin haka ne aka rahoto cewa 'yan sandan sun kama wasu daga cikin masu zanga zangar tunawa da waki'ar ENDSARS.

EndSARS: ECOWAS ta dauki mataki

A wani labarin, mun ruwaito cewa kotun kungiyar ECOWAS ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta take hakkin dan Adam a zanga-zangar EndSARS ta 2020.

Kotun ta ce gwamnatin ta ci zarafin Obianuju Catherine Udeh da wasu mutane biyu yayin zanga-zangar da aka yi zargin cewa an kasa akalla mutane 12.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.