Sankara: Kwamishina Ya Magantu kan Zarginsa da Hisbah Ke Yi, Ya Fadi Matakin Gaba
- Kwamishinan ayyuka na musamman a jihar Jigawa, Auwal Danladi Sankara ya musanta labarin da ake yadawa kansa
- Sankara ya ce an yada labarin zargin alaka da matar aure ne domin bata masa suna kawai da makiya ke yi
- Kwamishinan ya ce zai dauki matakin mai tsauri kan lamarin saboda an yi ne kawai domin zubar masa da mutunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Jigawa - Kwamishinan ayyuka na musamman a jihar Jigawa ya yi magana kan zargin da ake yi masa.
Auwal Danladi Sankara ya musanta labarin cewa an kama shi yana lalata da matar aure a jihar Kano.
Yadda Hisbah ta kama Kwamishina da zargin lalata
Punch ta ce kwamishinan ya ce an nemo tare da ya yada labarin ne domin bata masa suna amma babu kamshin gaskiya a ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta baku labarin yadda Hukumar Hisbah ta kama kwamishinan a cikin wani kango.
Darakta Janar na hukumar Hisbah, Dr. Abba Sufi ya ce sun cafke Sankara ne bayan korafi kan zargin lalata da matar aure.
Sufi ya ce kwamishinan zai girbi abin da ya shuka har ma da zargin siyar da magani ba bisa ka'ida ba, Daily Post ta tabbatar.
Sankara ya musanta zargin da ake masa
"Wannan labarin da ake yadawa cewa ina alaka da matar aure ba gaskiya ba ne, an yi haka ne domin bata mini suna kawai."
"A matsayina na mai aure, ina matukar mutunta hurumin aure kuma ba zan yi abin da zai zubar min da mutunci ba."
"Zan dauki wannan abu da muhimmanci wurin shiga shari'a da duk wadanda suka yada labarin domin bata mini suna."
- Auwal Danladi Sankara
Abubuwan sani game da Kwamishina, Auwal Sankara
Mun baku labarin cewa hukumar Hisbah na Kano sun cafke kwamishinan ayyuka na musamnan a jihar Jigawa, Auwal Ɗanladi Sankara ranar Jumu'a, 18 ga watan Oktoba.
Rahotanni sun bayyana cewa ƴan Hisbah sun damƙe kwamishinan ne bisa zargin lalata da wata matar aure a wani Kango a jihar Kano inda yanzu haka ya me hannunsu.
Asali: Legit.ng