Hukumar Hisbah a Kano Ta Yi Ram da Kwamishina kan Zargin Lalata da Matar Aure

Hukumar Hisbah a Kano Ta Yi Ram da Kwamishina kan Zargin Lalata da Matar Aure

  • Hukumar Hisbah a jihar Kano ta cafke wani kwamishina da ba a bayyana sunansa ba kan zargin lalata da matar aure
  • Rahoto ya ce Kwamishinan da ake zargi ya fito daga jihar Jigawa ya shige da wata matar aure cikin wani kango mallakinsa
  • Wani jami'in hukumar ya bayyana cewa an yi nasarar kama kwamishinan ne bayan zargin da mijin matar yake yi masu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Hukumar Hisbah a jihar Kano ta kama wani kwamishina kan zargin lalata da matar aure.

Ana zargin kwamishinan daga jihar Jigawa da ba bayyana sunansa ba kan shigewa wani kango da matar aure.

Hisbah ya cafke kwamishina da zargin lalata a Kano
Hukumar Hisbah ta kama wani kwamishina daga jihar Jigawa kan zargin lalata da matar aure. Hoto: Hisbah Command.
Asali: Twitter

Hukumar Hisbah ta kama kwamishina a Kano

Kara karanta wannan

Halin kunci: Gwamna a Arewa ya kafa kwamitin kayyade farashin kaya

Sai dai Daily Nigerian ta ce kwamishinan da aka kama na ayyuka na musamman ne mai suna Auwal Danladi Sankara a cikin kango mallakinsa bayan korafi daga mijin matar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani jami'i a hukumar Hisbah da ya bukaci a boye sunansa ya ce mijin matar yana zargin kwamishinan da neman matarsa, cewar The Guardian.

Wannan kame na zuwa ne bayan mijin matar mai suna Nasiru Bulama ya yi korafi ga Hisbah da kuma hukumar DSS.

Bulama a yayin shigar da korafin, ya ce yana zargin kwamishinan da mu'amala da matarsa, cewar rahoton The Nation.

Yadda aka cafke kwamishina da wata mata

"Korafin da Nasiru Bulama ya shigar akwai zargin lalata da kwamishinan ke yi da matarsa."
"Matar ta yi kokarin guduwa daga kangon lokacin da muka zo wurin inda ta buge mai gadi amma mun yi nasarar kama ta."

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya bayyana babbar matsalar Najeriya da Tinubu ya fara magancewa

- Cewar jami'in Hisbah

Sai dai har zuwa lokacin tattara wannan rahoto babu wata sanarwa ta musamman daga hukumar a hukumance kan lamarin.

Majalisa ta gabatar da kudirin inganta Hisbah

Mun ba ku labarin cewa Majalisar dokokin Kano ta yaba da ayyukan ƴan Hisbah, ta fara kokarin ƙara masu albashi da alawus-alawus a wata.

Ɗan majalisa mai wakiltar Minjibir, Abdulhamid Abdul ya gabatar da kudirin da ya nemi a maida ƴan Hisbah cikin ma'aikatan gwamnati.

Ya ce rundunar Hisbah ta Kano na taka muhimmiyar rawa wajen tsaftace jihar daga munanan ɗabi'u da kuma gyara tarbiyya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.