Peter Obi Ya Yi Magana da Jin Labarin Ibo Ya Zama Limami a Babban Masallacin Abuja
- Tsohon dan takarar shugaban kasa a inuwar LP, Peter Obi ya taya sabon limanin masallacin Abuja fatan alheri
- 'Dan siyasar ya bayyana nadin da wata manuniya kan jajircewa da jagorancin Iliyasu Usman ta bangaren addini
- Mista Peter Obi ya taya Farfesa Usman addu'ar nasara wajen sauke nauyin da ya rataya a kansa ta fuskar jagoranci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi ya bayyana fatan samun hadin kan yan kasar nan bayan nadin sabon limami.
A yau ne sabon babban limamin masallacin Abuja, Farfesa Iliyasu Usman ya kama aiki bayan mahukuntan masallacin sun amince da nadinsa.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, tsohon dan takarar ya bayyana fatan nadin zai zamo hanyar kara hada kan yan Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Peter Obi ya taya sabon limanin masallaci murna
'Dan takarar shugaban kasa a 2023, Peter Obi ya mika sakon taya murna ga babban limamin masallacin Abuja, Farfesa Iliyasu Usman.
Farfesa Usman shi ne ya zama dan kabilar Ibo na farko da zai yi limanci a babban masallacin, hakan ya ja hankalin jama'ar kasar nan.
Labarin nadin ya zo wa jama'a da dama da farin ciki, domin ana ganin zai kara hade kan musulmin Najeriya.
Obi: "Sabon limanin masallacin Abuja ya cacancanta
Peter Obi, wanda ya yi zawarcin kujerar shugaban kasar nan a 2023 ya ce sabon babban limanin Abuja, Farfesa Iliyasu Usman ya dace da jagorancin.
Mista Obi ya kara da cewa nadin da aka yi ya kara nuna kyawun jagorancinsa da ilimin addini da ya ke da shi, tare da addu'ar Allah ya dafa masa.
Limami ya haramta kudin shiga ittikafi
A baya mun wallafa labarin babban limanin masallacin Abuja, Ibrahim Maqari ya takawa masu karbar kudin shiga ittikafi a masallatai lokacin azumi burki.
Farfesa Ibrahim Maqari ya bayyana haka ne bayan an samu wani masallaci a Legas ya na yankewa masu ibada wasu kudi da za su biya kafin su shiga ittikafi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng