Direbobin da Ke Bin Babbar Hanya a Arewa Za Su Fara Biyan Haraji a sabon Tsari

Direbobin da Ke Bin Babbar Hanya a Arewa Za Su Fara Biyan Haraji a sabon Tsari

  • Ministan ayyuka, Sanata David Umahi, ya kaddamar da kwamitin aiwatar da tsarin karbar haraji a kan titin Abuja zuwa Keffi
  • Sanata Umahi ya bayyana cewa matakin kawo sabon tsarin karbar harajin na daga dabarun gwamnati na bunkasa titunan kasar
  • Gwamnatin tarayyar za ta kuma aiwatar da gina titin Keffi-Akwanga-Makurdi zuwa hannu biyu tare da karbar haraji a kansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta kaddamar da kwamitin aiwatar da sabon tsarin karbar haraji ta yanar gizo a kan babbar hanyar Abuja zuwa Keffi.

Kwamitin da ministan ayyuka, Sanata David Umahi ya kaddamar zai kuma aiwatar da gina titin Keffi-Akwanga-Makurdi zuwa hannu biyu.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare, gwamnatin Tinubu ta kawo karshen tallafin canjin kudi da na fetur

Ministan Tinubu ya yi magana kan fara karbar haraji a titin Abuja-Keffi a sabon tsari
Ministan Tinubu ya kafa kwamitin aiwatar da sabon tsarin karbar haraji a titin Abuja-Keffi. Hoto: @realdaveumahi
Asali: Twitter

Sabon tsarin karbar haraji kan titi

Ministan ya yi cikakken bayani game da sabon tsarin karbar harajin a ranar Alhamis yayin kaddamar da kwamitin a Abuja, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Umahi ya ce karbar harajin ba tare da rike tsabar kudi ba na daga cikin wani shirin hukumar kula da bunkasa manyan tituna (GDMI).

Wannan duk ya na cikin kokarin inganta harkar zirga-zirga a gwamnatin Bola Tinubu.

Jaridar The Punch ta rahoto Ministan ya ce:

"Wannan yana daya daga cikin manyan dabarun da shugaba Bola Tinubu ya dauka wajen ganin mun cimma muradun al’ummarmu a fannin bunkasa sufurin kasa.

Za a karbi haraji a titin Keffi-Makurdi

Ministan ya tariyo cewa bankin China Exim ne ya ba da kashi 85 na kudin da aka gina titin Keffi-Akwanga-Makurdi, sai gwamnatin taraya ta ba da kashi 15.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya bayyana babbar matsalar Najeriya da Tinubu ya fara magancewa

“Wani bangare na yarjejeniyar shi ne za su sanya haraji a kan titin sannan su mayar wa gwamnatin tarayya kudin domin ta biya bashin aikin.”

- David Umahi

Sanata Umahi ya kuma ce gwamnati za ta samar da kananun kasuwanni a kan hanyar inda matafiya za su rika siyayya ko shiga ban-daki idan bukatar hakan ta taso.

Gwamnati ta dawo karbar harajin 'toll gate'

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta amince da dawo da tsarin karbar kudin 'toll gate' daga masu ababen hawa a kan manyan titunan kasar.

Bayan shekaru ba tare da karbar harajin ba, mahukanta sun ce za a dawo da tsarin ne bayan shawarwari da masu ruwa da tsaki a ciki da wajen gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.