Tsohon Gwamna Ya Bayyana Babbar Matsalar Najeriya da Tinubu Ya Fara Magancewa
- Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Isa Yuguda ya kara jaddada yakininsa kan shirye shirye da manufofin shugaba Bola Tinubu
- Isa Yuguda ya shaidawa 'yan Najeriya cewa gwamnatin Tinubu za ta magance dukkanin kalubalen da kasar ke fama da su
- Misis Olu Verheijen, mai ba Tinubu shawara kan makamashi ta fadi yadda fannin mai da gas ke da muhimmanci a kasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Malam Isa Yuguda, tsohon gwamnan Bauchi ya bayyana cewa gwamnatin Bola Tinubu za ta ceto Najeriya daga kalubalen da ta dade tana fama da su.
Yuguda wanda kuma shi ne shugaban kwamitin amintattu na kungiyar APC-ACPPF, ya bayyana haka ne bayan wani taro da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis.
"Bola Tinubu ya gyara lantarki" - Yuguda
Tsohon gwamnan ya yabawa manufofin shugaban kasar, musamman a bangaren wutar lantarki, a matsayin wani abin fatan alheri ga kasar nan, inji rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Isa Yuguda, gwamnatocin da suka gabata sun zuba jari sosai a fannin samar da wutar lantarki ba tare da samun nasara ba.
Duk da haka, ya yaba da matakan da gwamnati mai ci ta dauka da suka fara daidaita fannin rarraba wutar lantarki tare da samar da ita ga mafi yawan jama'a.
"Gwamnati ta aiwatar da manufofi na inganta rarraba wutar lantarki da kuma samar da ita a araha ga mafi yawan 'yan kasar nan, lamarin da ya kamata a yaba mata sosai."
- Isa Yuguda.
Gwamnati ta yi magana kan fannin mai
Tun da farko, Misis Olu Verheijen, mai ba shugaban kasa shawara kan makamashi, ta bayyana mahimmancin fannin mai da iskar gas a ga tattalin arzikin Najeriya.
Ta yi nuni da cewa, fannin ya samar da 90% na kudaden da ake samu daga waje.
Olu Verheijen ta ce gas yana da matukar muhimmanci wajen daidaita Naira da kuma dakile hauhawar farashin kayayyaki.
Verheijen ta bayyana cewa gwamnati ta samar da dala miliyan 600 na hannun jari a bangaren makamashi a cikin 2023, biyo bayan umarnin shugaba Tinubu.
"Tinubu na kokarin kawo gyara" - Yuguda
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon gwamnan jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda ya ce ba shugaban kasa Bola Tinubu ne ya jawo tsadar rayuwa ba.
Isa Yuguda wanda ya ce shi ma Tinubu gadar tsadar rayuwar ya yi daga gwamnatin baya ya kuma ce gwamnati mai ci na iya kokarinta na kawo gyara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng